ZABEN FIDDA GWANI: APC ta yi barazanar hukunta wadanda ba su janye kara a kotu ba

0

Jam’iyyar APC ta soki mambobin ta wadanda suka garzaya kotu domin neman hakkin su bayan gudanar da zabukan fidda gwani na jam’iyyar.

Wannan suka da barazana da APC ta yi, ta zo ne a daidai lokacin da rigingimu a kotuna da dama a fadin kasar nan suka dabaibaye APC sakamakon yadda jam’iyyar ta gudanar da zabukan fidda gwani.

Mambobin jam’iyyar a jihohi irin su Imo, Delta, Ogun, Rivers da wasu jihohi duk sun garzaya kotu domin kalubalantar yadda aka yi musu rashin adalci a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a farkon watan Oktoba.

Kakakin jam’iyyar APC na kasa, Lanre-Issa Onilu, ya bayyana a ranar Litinin cewa gaggawar garzayawa kotu ba ita ba ce hanyar neman warware matsala, tunda jama’iyya ta na da kwamitin ta na sasantawa da warware matsalolin da suka shafin jam’iyya.

Ya ce abin da suka yi ba wani abu ba ne, sai saba wa jam’iyya da kuma rashin da’a. Ya kara da cewa yi wa jam’iyya kafar-ungulu ne, domin kararrakin da suka kai ya saba da dokokin jam’iyyar APC.

Daga nan sai ya shawarce su da su janye kararrakin da suka kai, ko kuma jam’iyyar ta dauki mataki a kan su.
Ya ce janyewar ta su zai sa su ci gajiyar sasanyawar da kwamiti ya fara domin a dinke duk wata baraka a yanzu.

Share.

game da Author