Kungiyar yi da kai na ‘Youth Initiative for Advocacy Growth and Advancement (YIAGA)’ ta yi tir da zabukan cike gurbin da aka yi a jihohin Katsina, Bauchi da Kwara a ranar Asabar din da ta gabata.
Shugaban kungiyar Samson Itodo ya bayyana cewa ba a gudanar da wadannan zabuka cikin bin dokar zabe ba.
Sakamakon zabukan da hukumar zabe ta sanar bayan zabukan a wadannan jihohi jam’iyyar APC ce ta yi nasara inda tayi wuji-wuji da sauran jam’iyyun da suka fafata a zaben.
Itodo yace wadannan zabuka basu kusa da zaben da za ayi masa shaidar nagarata ba.
“ An yi amfani da jami’an tsaro wajen muzguna wa masu zabe sannan kuma a wasu mazabun an yi ta hadahadar siyan kuri’u ne kawai daga mutanen gari.
A cewar Itodo gaba daya zabukan ba a yi su cikin fasali ba. An samu wadanda basu kai su yi zabe ba suna jefa kuri’a sannan wasu daga baya suka zo rumfunan zaben kuma aka bar su susa kada kuri’a.
Wata jami’ar kungiyar Cynthia Mbamalu ta yi kira ga hukumar INEC da ta koma teburin ta natsu domin ganin irin haka bai sake faruwa ba musamman ganin cewa ana gab da a yi zaben duk kasa nan ba da dadewa ba.
Discussion about this post