Kungiyar nan Mai Hada Maharawa a Kafafen Yada Labarai ta Najariya, ta sa ranar da za a gudanar da mahawara tsakanin masu takarar shugaban kasa a zaben 2019.
Sanarwar ta ce za a yi mahawa tsakanin masu takarar mataimakin shugaban kasa a ranar 14 Ga Disamba, 2018, yayin da za a tafka mahawara a tsakanin masu takarar shugaban kasa a ranar 19 Ga Janairu, 2019.
Za a gudanar da mahawarar ce a Otel din Hilton, Abuja.
Mahawarar za ta fi karfi ne kacokan a kan tattalin arziki, wutar latarki, samar da aikin yi, harkokin kiwon lafiya, tsaro da sauran su. Haka masu shirya mahawarar suka bayyana.
Sai dai kuma ba a tabbatar ba ko manyan ‘yan takara sun nuna amincewar shiga mahawarar ba.
A wadda aka shirya kafin zaben 2015 dai Buhari bai shiga ba, amma Goodluck Jonathan ya shiga.
Sai dai kuma shugaban wannan kungiya mai suna Jimoh Momoh, ya yi kira da a kafa dokar da za ta tilasta wa kowane dan takara fitowa a tafka mahawara da shi, domin ya bayyana wa masu zabe irin kamun ludayin da za ya yi wa mulkin sa idan har ya yi nasara.