Za mu maida hankali wajen ganin an ci gaba da yin rigakafi a jihar Yobe – Gaidam

0

Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta zage damtse wajen ganin an ci gaba da yin allurar rigakafi a jihar.

Gaidam ya fadi haka ne da yake ganawa da gidauniyar Bill da Melinda Gates da gidauniyar Dangote.

Ya ce gwamnati dole yanzu gwamnati ta maida hankali wajen ganin an dawo da yin rigakafi gadan-gadan a jihar tunda an dace da dawowar zaman lafiya a jihar.

” Ina tabbatar muku da cewa zaman lafiyar da muka samu zai taimaka wajen gano yara da matan da ba a yi musu allurar rigakafi ba tun a da.

Gaidam ya kuma yi kira ga gidauniyar Bill da Melinda Gates da gidauniyar Dangote kan ci gaba da tallafawa jihar game da haka.

A karshe shugaban gidauniyar Bill da Melinda Gates, Bill Gates da jami’ar gidauniyar Dangote Zuwaira Yusuf sun jinjina wa kokarin samar da zaman lafiyar da gwamnatin jihar Yobe ke yi. Sannan sun hore gwamnatin da ta ci gaba da haka musamman yanzu da za a dawo da yin allurar rigakafi a jihar.

Share.

game da Author