Jami’in hukumar masu yi wa kasa hidima (NYSC) David Markson ya bayyana cewa za a horar da daliban da za su yi wa kasa hidima a jihohin Barno da Yobe a jihar Gombe.
Markson ya sanar da haka a takarda da ya fito daga ofishin sa a Gombe wanda jami’ar hulda da jama’a Magaret Dakama ta saka wa hannu ranar Litini.
Ya ce jimlar daliban da NYSC za ta horas a jihar Gombe sun kai 1,700 sannan za a fara yi musu rajista daga ranar 15 zuwa 18 ga watan Nuwamba.
A karshe Markson ya hori mazaunan garin Gombe da masu motocin haya kan tallafa wa dalibai da za a horar da su a jihar musamman yadda mafi yawan su baki ne da basu san gari ba.