Za a ba fara kula da mata masu ciki kyauta a asibitocin jihar Bayelsa

0

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara shirin samar wa mata masu ciki kula kyauta a asibitocin jihar.

Dickson ya fadi haka ne a babban birnin jihar Bayelsa, Yenagoa a taron kaddamar da wannan shiri na gwamnati.

Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin ta rage yawan mace-macen mata da jarirai a jihar.

” Sannan shirin zai taimaka wajen hana mata zuwa wajen ungozoma na gargajiyya domin hahuwa.

Dickson ya ce daga yanzu duk mace mai cikin da ta yi rajista da asibiti za ta rika samun Naira 3000 duk wata domin samun kudin motar zuwa asibiti.

Ya kuma ce za a hada su tare da wasu kayayyaki da mata masu ciki kan bukata domin bunkasa kiwon lafiyar su da na dan dake cikin su.

A karshe Dickson yace haka za a ci gaba da yi har sai mace ta haihu.

” A yanzu dai mata 1000 ne suka fara amfana da wannan shiri.” Inji Dickson.

Share.

game da Author