YUNWA: Kano da UNICEF sun hada kai domin ceto kananan yara a jihar

0

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta saka hannu a takardar yarjejeniyya na hada guiwa da asusun tallafa wa yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin kula da yaran dake fama da matsanancin yunwa a jihar.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kabiru Getso ya saka hannu a takardar a madadin gwamnatin jihar sannan jami’in UNICEF Mohamed Fall ya saka hannu a madadin UNICEF.

A bayanan sa Getso ya ce gwamnati za ta hada hannu UNICEF domin samar da magunguna sannan UNICEF daga nata aljihun za ta samar da mafi yawa daga cikin magungunan da ake bukata don kula da yaran dake fama da matsanancin yunwa.

‘‘A takaice dai UNICEF da gwamnatin jihar Kano za su samar da magunguna daya kai 24,000 kenan domin kula da yaran dake fama da matsanancin yuwa a jihar. Inji Kwamishina Getso.

Share.

game da Author