Wani likita dake aiki da asibitin Calvary Estate dake garin Benin, jihar Edo, Osas Ikponwonsa ya yi kira ga mata da su rage yawan shan magungunan musamman wadanda ke dauke da sinadarin ‘Estrogen’ domin guje wa kamuwa da kabar ciki.
Osas ya bayyana cewa ‘Estrogen’ sinadari ne dake taimakawa wajen kara wa farjin mace mata da wasu bangaron jikin ta lafiya. Sannan wannan sinadarin ya fi yawa a kwayoyin hana haihuwa.
Sannan kaban ciki cuta ce dake fito a mahaifar mace wanda idan ba a gane da wuri ba ke iya hana mace haihuwa.
Osas ya ce har zuwa yanzu likitoci basu gano abin dake kawo wannan cuta ba saidai bincike ya nuna cewa yawan amfani da magunguna na daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar.
” Yawan rashin lafiya a lokacin da mace ke haila, yawan zuban jini a lokacin haila, ciwon ciki, jin nauyi a mara da sauran su na cikin alamun wannan cuta.
Osas ya ce bincike ya nuna cewa kashi 20 zuwa 50 na matan dake a duniya na dauke da wannan cuta. Sannan wasu matan kafin su kai shekarun gama haihuwa kashi 30 zuwa 77 daga cikin sukan kamu da wannan cuta a duniya.
A dalilin haka Osas yake kira ga mata da su guji shan magani batare da izinin likita ba musamman wadanda ke dauke da sinadarin ‘Estrogen’ domin gujewa kamuwa da cutar.