‘Yan sanda sun kashe barayin shanu 104 a jihar Zamfara

0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kashe barayin Shanu 104 a batakashi da suka da su a dazukan Birnin Magaji dake jihar Zamfara.

Moshood Jimoh da ya sanar wa manema labarai bayanan wannan artabu da suka yi da wadannan ‘yan ta’adda yace an kama mutane 85 sannan an kwato bindigogi kirar AK 47 27, da wasu kirar hannu.

” Barayi irin haka sun hana mazaunan kauyen Birnin Mogaji sakat da sace sacen amfanin gona da dabbobi inda a dalilin haka rundunar ‘yan sandan jihar ta aika da ma’aikatan ta kauyen domin kawo karshen haka.”

Bayan haka kuma an kwato shanu sama da 250 da tumakai sama da 100. Moshood yace duk an maida wa masu shi abin su.

Share.

game da Author