Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta gabatar wa manema labarai da wata jami’ar asibiti mai suna Fatima Suleiman da kuma wani boka mai suna Salaudeen Ibrahim, bayan an damke su bisa zargin mahaifar wani jinjiri sabuwar haihuwa.
An ce sun hada baki sun sace mahaifar ce a asibitin Capstone, a ranar 31 Ga Oktoba, a Ilorin.
Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar, Aminu Saleh ne da kan sa ya yi wa manema labarai jawabi a hedikwatar su da ke Ilori, inda ya ce an damka mahaifar ce ga Suleiman, domin ya bai wa mahaifin jinjirin, mai suna Jimoh Ibrahim, bayan da aka yi wa mahaifiyar sa, Bashirat Jimoh fita a lokacin haihuwar ta.
Maimakon a damka masa mahaifar, sai ita jami’ar asibitin ta kai wa bokan domin a yi asirin samun kudi da ita.
Kwmishina ya ce Fatima ta kai wa boka mahaifar da nufin samun ladar kudade masu yawa daga hannun sa.
Ya ce da an kammala bincike za a maka su kotu.