Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR ta bayyana cewa akwai sama da masu gudun hijira 30,000 da suka tudado daga kasar Kamaru, saboda kokarin kauce wa fadace-fadacen da ke faruwa yankin kasar masu magana da Turancin Ingilishi.
Kakakin Hukumar, Babar Baloch ne ya bayyana haka kuma ya na mai nuni da cewa aikin daukar dawainiyar masu gudun hijira na kokarin gagarar adadin gudummawar da ake bayarwa wajen kulawa da su.
Baloch ya ce rahotanni na nuni da cewa akwai jama’a da dama na ta fantsamowa cikin Najeriya daga yankin Kamaru mai magana da yaren Turancin Ingilishi, sakamakon tashin hankalin da ke faruwa a yankin.
Ya kuma yi karin hasken cewa kashi 80 bisa 100 na masu shigowar duk mata ne da kananan yara, wadanda al’ummomin Kudu maso gabacin Najeriya ke ta bas u mafaka da matsugunai.
UNHCR ta ce hukumar na kokarin tattara su wuri daya a a matsugunai daban-daban a jihohin Cross-River da Benuwai, domin samun saukin kulawa da ba su tsaro da kuma samar masu ababen rayuwa na yau da kullum.
Discussion about this post