A dalilin shirin fara yajin aikin gama gari da kungiyar Kwadago ta kira da za a fara daga ranar 6 ga watan Nuwamba, an dan fara samun layin motoci a gidajen saida mai dake jihar Kano.
A karamar hukumar Gwarzo, an ga motoci suna tsaye a gidajen mai domin siyan man fetur. Wasu da dama daga gidajen saida man fetur din sun kulle gidajen cewa wai a dalilin kishi-kishin din da aka ji wai za a rage kudin mai shine yasa ba su sayo man ba tukuna.
Ko da yake gidajen mai a cikin garin Kano na saida mai.
Shugaban kungiyar masu hada-hadar man fetur reshen jihar Kano Bashir Dan-Malam, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai cewa wannan karanci da aka fara samu a jihar na da nasaba da rade-radin rage kudin mai da ake da yada wa.
Ya ce wasu na ganin kamar gwamnati za ta rage kudin mai daga naira 145 zuwa naira 95 kowace lita.