Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, wanda ya fice daga APC ya koma PRP, ya bayyana dalilan da suka sa mambobin majalisar dattawa na APC suka biris daga kulle-kullen neman tsige Saraki.
Sanatan ya ce sun ki tsige Saraki, saboda tsige shi din dai bai halasta ba a ka’idar dokar Najeriya, wadda da ita kowa ke tinkaho a kasar nan.
Bacin bai halatta ba, Shehu Sani ya ce babban dalilin dai shi ne, babu ta yadda za a yi su iya tsige Saraki a bisa ka’idar da doka ta tanadar.
Da ya ke ganawa da manema labarai jiya Lahadi a Abuja, Sani ya ce saboda ‘yan APC ba su da yawa ko rinjayen adadin da doka ta ce za su iya kaiwa su tsige Saraki.
Dama kuma shugaban APC, Adams Oshiomhole ne ya rika tayar da jijiyoyin wuya ya na kartar kasa cewa sai an tsige Saraki ko da karfin tuwo, ko kuma ya yi murabus tun kafin a tsige shi.
Saraki ya ki amincewa ya sauka, su kuma Sanatoci sai suka watsar da batun cire shi, tun bayan da suka dawo daga dogon hutun sati goma.
“Ina tabbatar muku da cewa APC sun so su tsige Saraki, amma sun watsar da shirin ne kawai saboda sun ga cewa ba su da yawan da za su iya tsige shi, kamar yadda doka ta tanadar kawai.”
” Sannan kuma Saraki mutum ne da ke tafiya da kowa ba tare da ko kana dan wani jam’iyya ba. Sannan kuma ‘yan jam’iyyar APC basu da hadin kai kamar yadda sanatocin PDP ke da. Su sanatocin PDP a daure suke uwri daya tamau sannan haka kawai ba zaka iya sakowa ka nemi wargaza su ba.”
Discussion about this post