Yadda rahoton PREMIUM TIMES ya sa aka damke dan takarar gwamnan APC a filin jirgin sama

0

Jami’an tsaro sun damke Sanata Hope Uzodinma, dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, a bisa zargin sa da damfarar gwamnati dala milyan 12.5.

Hope Uzodinma, wanda ya na daga cikin ‘yan takarar gwamna a jihar Imo na APC da ke tankiya da juna a kotu a yanzu haka, an damke shi ne a filin jirgin sama na Laos, jim kadan bayan dawowar sa daga wata tafiya da ya yi kasashen waje.

Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa mai Kwato Kadarorin Sata, Okoi Obono-Obla, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kama Uzodinma kuma ya na tsare a Asokoro, Abuja.

“Kusan shekara daya kenan ana kokarin kama shi, amma ya na zillewa. Sai yau ya shigo hannu.” Inji Obla.

Obla ya ce kwamitin sa ya tsunduma neman Uzodinma tun bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa yadda aka bai wa sanatan kwangilar naira bilyan 26 a lokacin gwamnatin Jonathan. An damka masa kudin somin-tafi na dala milyan 12.5, ya karba amma har yau bai ko fara kai diga da cebur a wurin aikin ba.

Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ce a lokacin ta ba shi kwangilar yashe mashigar jiragen ruwa ta tashar Kalaba, amma ya yi awon-gaba da kudaden.

Haka nan kuma a rahoton da PREMIUM TIMES ta bayar a can baya, ta ruwaito yadda aka ba shi kwangilar ba tare da cika sharudda ba, ko kuma aka ba shi kwangilar tare da kin yin amfani da sharuddan da ya kamata a cika kafin a bayar da kwangilar.

Obla ya ce kwamitin sa ba ya tsare wanda ake zargi har wani tsawon lokaci. Don haka a cewar sa, da zaran sun gama bincike, kuma Uzodinma ya rubuta bayani, za a maka shi kotu kawai.

Ya yaba da rahoton da PREMIUM TIMES ta buga a shekarar da ta gabata, wanda ya fallasa harkallar da Uzodinma ya tafka, ya na mai cewa sanatan a dibga laifin cin amanar karya tattalin arzikin kasa.

Uzodinma shi ne ke rigima da daya dan takarar gwamnan jihar Imo, Nwosu, wanda ke auren ‘yan gwamna na yanzu, Rochas Okorocha.

Amincewar da APC ta yi cewa Uzodinma ne dan takara, ya haddasa rigima tsakanin Okorocha da Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Share.

game da Author