Yadda Obama ya shirya tuggun kayar da ni zaben 2015 – Goodluck Jonathan

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya ragargaji tsohon shugaban Amurka Barack Obama, inda ya bayyana kamalan da Obama ya aiko wa ‘yan Najeriya kusa ga zaben 2015 da cewa shisshigi ne, wuce-gona-da-iri da kuma mummunar aniya dankwafar da gwamnatin Jonathan din.

Jonathan ya ce Obama ya nuna masa bambanci da bangaranci karara a lokacin da ya aiko da wasika ta faifan bidiyo ana kusa da zaben 2015, inda ya roki ‘yan Najeriya kuma ya shawarce su a kan shugaban da ya kamata su zaba.

Jonathan ya bayyana haka a cikin littafin sa da aka kaddamar yau Talata a Abuja. Ya ce a ranar 25 Ga Maris Obama ya aiko da sakon ta bidoyo ga ‘yan Najeriya.

“A cikin sakon, Obama ya sahawarci ‘yan Najeriya da su bude sabon babi a zaben da za su yi. Wanda duk ya san salon magana da zaurance ko hannun-ka-mai-sanda, to ya san Obama na nufin a zabi jam’iyyar adawa a lokacin.”

PREMIUM TIMES ta mallaki littafin tun kafin a kaddamar da shi, duk kuwa da irin tsauraran matakan da Jonathan da kuma makusantan sa suka dauka.

An dai shirya gudanar da zaben 2015 a cikin watan Fabrairu, 2015, amma kuma sai aka daga zaben zuwa cikin watan Maris, 2015.

Makonni shida da aka kara wajen dage zaben ya janyo hayaniya da cece-ku-ce matuka, inda aka zargi Jonathan da yunkurin kitsa tuggun da zai ci gaba da mulkin Najeriya.

Sai dai kuma Jonathan ya ce ba shi kadai ba ne ya yanke shawarar a dage zabe, har da shawarar tsoffin shugabannin kasar nan, bayan da aka samu rahotannin daga hukumomin tsaron kasar nan.

“Sakon da Obama ya aiko ya yi tasiri sosai, kai ka ce gaba dayan ‘yan Najeriya ba su san ba su ma san abin da ya dace su yi ba, sai sun jira Obama ya sa su a hanya.

Ya kwankwatsi kan Obama sosai, wanda ya ce ya rika babatun wai tilas ‘yan Najeriya su yi zabe ba tare da wata barazana ba, amma kuma shi Obama din bai yi wata rawar gani ba wajen taya Najeriya ta kori Boko Haram kafin zabe.
Hae ila yau, Jonathan ya soki tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry, wanda ya ce duk da kokarin da Najeriya ta yi domin ta gamsar da shi dalilan dage zaben 2015, hakan bai gamsar da Kerry din ba.

“Ta yaya Sakataren Amurka zai dauka cewa sun fi gwamnatin Najeriya damuwa da ‘yan Najeriya. Don me Amurka za ta kasa fahimtar hadarin gudanar da zaben a yanayin da Boko Haram ke rike da mafi yawan yankin Arewa maso Gabas na kasar nan?

“Duk da alkawari da alwashin da aka nuna masu cewa ranar 29 Ga Mayu, 2015 za a bada mulki ga wanda ya yi nasara, hakan bai gamsar da su ba. Ga shi kuma an nuna musu cewa dokar Najeriya ba ta bada damar a kara ko da yini daya daga ranar 29 Ga Mayu ba.”

Share.

game da Author