Yadda Gwmanatin Buhari ta karkatar da naira biliyan 378 ta rike biyan kudin tallafin mai a boye

0

Wasu muhimman takardu da suka fado hannun PREMIUM TIMES, sun tabbatar da yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta zaftari naira biliyan 378 daga cinikin gas a asusun NLNG, ta biya kudaden tallafin man fetur da su, wato ‘subsidy’.

Karkatar da wadannan kudade ya zo ne a daidai lokacin da ake zargin Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur, karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari ta ware wasu zunzurutun kudade har dala biliyan 3.5 na biyan tallafin man fetur da ta ke kashewa afujajan, ba tare da amincewar Majalisar Tarayya ba.

Hakan laifi ne kuma take dokar kasa ce gwamnatin tarayya ta yi ko kuma ta ke kan yi.

Gwamnatin Buhari dai tun kafin ta hau mulki, jam’iyyar APC ta yi alkawarin rage kudin litar man fetur idan ta kafa gwamnati.

Sai dai kuma maimakon a samu ragi daga naira 87 da ta taras da litar fetur daya, sai ta kara farashi zuwa 145, a bisa dalilin cewa gwamnati ta na biyan kudin rarar fetur ga manyan dillalai.

Kara wa fetur kudi ya sa gwamnati ta ce ta soke biyan dillalan fetur kudin tallafin tsadar mai, haka su ma dillalan akasari sun daina shigo da mai, sai dai gwamnati ce ke shigo da shi.

Cikin watan Oktoba ne Dan Majalisa daga Biodun Olujimi, dan PDP daga jihar Ekiti ya tayar da cacar baki a zauren majalisa, inda ya yi ikirarin cewa akwai wasu kudade har dala biliyan 3.500 da NNPC ke kashewa, ba tare da iznin majalisa ba.

Sai dai kuma NNPC ta ce ba ta da wadancan kudade da aka yi zargi, amma ta na da dala bilyan 1.05 da ta ke amfani da su wajen saisaita hada-hadar raba fetur a fadin kasar nan da kuma ayyukan jigilar shigo da shi.

Yayin da a baya kakakin yada labarai na NNPC, Ndu Ughamadu ya ce daga kungiyoyin kasashen waje aka samu kudaden, sai kuma ga shi Shugaban Kamfanin NNPC, Maikanti Baru a makon da ya gabata ya ce an zaftari kudaden ne daga asusun NLNG, wato kudaden gas.

Takardun bayanai da suka fado hannun PREMIUM TIMES sun nuna yadda aka zaftari kudaden a tsakanin watan Disamba, 2017 zuwa cikin Janairu na 2018, aka karkatar da kudaden wajen biyan tallafin kudaden jigilar man fetur, wanda gwamnati ta soke biya, tun bayan da aka yi karin fetur daga naira 87 zuwa naira 145.

Kafin a taba wadannan kudade kuwa, dokar kasa ta ce sai Shugaban Kasa ya tuntubi Majalisar Dattawa, Majalisar Tarayya da kuma Majalisar Dokoki na Jihohi, domin tarayya da jihohi na da hakki a cikin kudaden.

Sai dai kuma gwamnatin Buhari ba ta yi haka ba.

Shugaban Kamfanin mai na kasa, Maikanti Baru ya shaida wa majalisar dattawa a makon da ya gabata cewa ma’akatar sa bata yi amfani da irin wadannan kudade da ake ta cece-kuce a kai ba. Sannan ma’aikatar ta bayyana cewa ita da kanta majalisar dattawa ne ta ba ta damar nemo duk hanyar da za a warware wahalar mai da aka yi fama dashi a karshen shekarar bara.

Sai dai kuma majalisar ta ce ba ita ce ta ba kamfanin mai din damar ta wuwuri irin wadannan kudade don biyan tallafin rarar man fetur a wancan lokacin ba.

Share.

game da Author