A cikin watan Afrilu da ya gabata ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gaggawar kwasar dala miliyan 469.4 ya biya gwamnatin kasar Amurka, domin yarjejeniyar sayo jiragen yaki 12 daga Amurka.
An kulla yarjejeniyar cewa gwamnatin Amurka ce za ta bada kwangilar sayen jiragen ga wani kamfanin kera jiragen yaki na kasar, mai suna Sierra Nevada.
Za a sayi jiragen yaki 12 samfurin A-29 Super Tucano, sannan kuma duk a cikin kudin kwangilar, za a rika bayar da horo ga sojojin Najeriya wadanda za su rika tukawa da sarrafa jiragen har tsawon shekaru uku.
MATSALOLI DA ALAMOMIN TAMBAYA A KWANGILAR
*Duk da cewa tun cikin watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya kwashi kudaden ya bai wa gwamnatin Amurka, har dala miliyan 469.4, kwatankwacin naira bilyan 168.8, sai cikin wannan makon ne Ma’aikatar Tsaro ta Gwamnatin Amurka ta bada sanarwar bayar da kwangilar fara kera jiragen.
An yi gaggawar kwasar kudaden ba tare da amincewar Majalisar Dattawa ba. Duk da hakan ya kawo cece-ku-ce, jama’a da dama sun bai wa Buhari uziri, ganin cewa an yi cinikin a gaggauce, domin shawo Kn matsalar Boko Haram da ke fafata yaki da sojojin Najeriya.
Guyawun wasu da dama sun fara sarewa, yayin da gwamnatin Buhari ta bayyana cewa jiragen da cinikin biya ka dauki kayan ka ba ne, sai an jira an kera su. Sannan kuma sai cikin 2020 za a kammala kawo su Najeriya.
Kwanan nan kuma Ma’aikatar Tsaron Amurka ta ce an rattaba yarjejeniya da Sierra Nevada masu kera jirgin cewa sai cikin shekarar 2024 za su kammala kera jiragen, wadanda za a kera a birnin Jacksonville.
Sanarwar da Amurka ta yi, ta ce kwangilar ba ta wuce a kan kudi dala miliyan 344.7 ba.
Shi kuma Buhari ya ce akan dala miliyan 468.4 aka bada kwangilar, kuma haka aka bai wa gwamnatin Amurka, wadda ta tsaya wa Najeriya wajen wakilcin bayar da kwangiar.
Yanzu ta fito fili cewa sai nan da shekaru shida za a kammala kera wasu jiragen kenan, ba kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta rika yadawa ba.
An yi aringizon tsabar kudi har naira biliyan 43.5 a cinikin jiragen guda 12.
Buhari ya ce ya bai wa Amurka dala milyan 469, ita kuma Amurka ta ce an ba ta dala milyan 344, kamar yadda kudin kwangilar ya ke a rubuce.
An bayar da kwangilar a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke yayata cewa ta gama da Boko Haram.
Jiragen ba za su yi amfani ba kenan, a yanzu, lokacin da aka fi bukatar su, ganin yadda Boko Haram suke yawan kai wa sansanin sojoji hari.