Wasu dake dauke da muggan makamai sun mamaye garin Tangaza, Jihar Sokoto

0

Kungiya da ba a san ko wacce iri ba ce ta mamaye karamar hukumar Tangaza, dake jihar Sokoto.

Kungiyar dai har sun fara karbar haraji daga mazauna wannan gari.

An ce wadannan ‘yan kungiya sukan bi gida-gida suna karbar haraji daga mazauna garin Tangaza da kauyukan dake zagaye da garin ba tare da wani ya iya ce musu komai ba har yanzu.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa wadannan mutanen ya ce suna kama da mutanen kasar Nijar, sannan suna nada rawani a kawunan su dauke da manyan bindigogi. ” Sun mamaye garin Tangaza har sun fara matasa sojojin haya, wato matasa suna horas dasu dabarun yaki a karshe su basu sabbin babura”

” Kowani makiyayi na biya wa shanun sa naira 500 sannan tumakai kuma naira 200. Bayan haka suna hukunta makiyayan da ke fadawa gonakin manoma sannan su dora musu tara.

Shi dai wannan gari na Tangaza da kauyukan da ke zagaye da na da iyaka da wasu garuruwan kasar Nijar da har ma auratayya kan hada su.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa yanzu haka yana hanyar sa na zuwa.

Share.

game da Author