Wanke Ido da fitsari baya warkar da ciwon Ido ‘Apollo’

0

Ciwon Ido da ake kira ‘Apollo’ ciwon ido ne dake kama mutane sannan nan da nan sai kaga ya yadu.

Alamomin da ke nuna an kamu da cutar sun hada da kaikayin ido, hawaye, yawan kwantsa,ido yayi ido, zafi a ido, ciwon kai da sauran su.

Gwanaye sun ce kamata ya yi da zaran an kamu da wannan cutar a garzaya zuwa asibiti domin samun kulan da ya kamata.

Sun ce za a iya wanke ido da ruwa mai tsafta ko kuma a kara kan kara a ido domin samun saukin radaddin zafin da ake ji sannan a nemi taimakon likita.

Likitocin sun bayyana wasu hanyoyin da mutane za su iya kiyayewa domin guje wa kamuwa da wannan cutar.

1. Mutane su guji barin kura ko kuma tsakuwa na shiga idanuwan su.

2. A guji duk hanyoyin da aka san za a iya kamuwa da mura.

3. A daina shiga cikin mutane idan aka kamu da wannan cuta.

4. Fesa turarai a ido na cutar da ido.

5. A daina Wanke ido da ruwan toka, fitsari da amfani da tozali a ido a lokacin da aka kamu da wannan cutar.

6. Amfani da kayan wanda ya kamu da cutar kama tabarau, tozali da sauran su na na sa a kamu da cutar.

Share.

game da Author