Wadanda ke dauke da cutar Kanjamu 360,000 za su mutu zuwa shekarar 2030 – UNICEF

0

Jami’ar asusun (UNICEF) Henrietta Fore ta bayyana cewa mutane 360,000 dake dauke da cutar Kanjamu a duniya za su mutu zuwa shekarar 2030.

Fore ta bayyana cewa UNICEF ta gano haka ne a bincike da ta gudanar game da aiyukkan hana yaduwar cutar da kasashen duniya ke yi.

Ta ce sakamakon bincike ya nuna cewa har yanzu akwai sauran aiki da ya kamata kasashen duniya su maida hankali a kai.

Fore ta ce binciken ya kara nuna cewa za a sami raguwa a adadin yawan yara da manyan dake mutuwa sanadiyyar kamuwa da kanjamau a 2030.

Share.

game da Author