USAID ta raba gidajen sauro miliyan 3.3 a jihar Akwa Ibom

0

A ranar Talata ne ofishin jakadancin kasar Amurka ta bayyana cewa USAID ta tallafa wa fannin kiwon lafiyar jihar Akwa Ibom da gidajen sauro miliyan 3.3.

Ofishin jakadancin ta bayyana cewa gidajen sauron da USAID ta raba ya kai na dala miliyan 9.7 sannan za a raba gidajen sauron ne a duk kananan hukumomin dake jihar.

USAID ta raba wadannan gidajen sauron ne domin kare mutane daga kamuwa da zazzabin cizon sauro musamman yadda bincike ya nuna cewa zazzabin ya kashe mutane 107,000 a Najeriya a shekarar 2016.

” Zazzabin cizon sauro cuta ce da aka fi kamuwa da ita a lokacin damina sannan amfanin da wadannan gidajen sauron musamman da dare zai kare mutane daga kamuwa da cutar.

A karshe ofishin jakadancin ta ce USAID za ta raba irin wadannan gidajen sauro a jihar Bauchi a cikin watan Nuwamba.

Share.

game da Author