TSAKANIN BUHARI DA ATIKU: Kowa Ta Sa Ta Fisshe Shi: Tsokaci 40 Game Da Zaben Shugaban Kasa

0

Yau Lahadi ne dukkan ’yan takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019 za su fara fafata yakin neman zabe gadan-gadan. Koda ya ke sai dai a ce za su kaddamar, domin dukkan su sun fara yakin ko dai a fakaice, ko a karkashin kasa ko kuma ta yadda ‘yan Najeriya ke ta bayyana ra’ayoyin su a kafafen yada labarai, soshiyal midiya, wuraren taruka, fastoci, majalisin matasa da na dattawa a unguwanni, tashoshin mota har ma da teburan mai shayi.

*Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ce ta bayar da iznin a fara gudanar da kamfen daga ranar Lahadi, 18 Ga Nuwamba, 2018. Amma wannan izni ya na kan masu takarar shugaban kasa ne da kuma majalisar tarayya kadai.

*Sama da jam’iyyu 50 ne suka shiga takarar shugaban kasa, amma an maida hankali ne kacokan a kan jam’iyyar APC mai rike da mulki da kuma PDP, babbar jam’iyya mai adawa. Ana sa ran cewa daga cikin wadannan jam’iyu biyu ne shugaban kasa zai fito. Ko dai Muhammadu Buhari dan takarar APC, wanda ke kan mulki a yanzu, ko kuma tsohon Mataimakain Shugaban Kasa, Atiku Abubakar na PDP.

KO GUGUWAR BUHARIYYA ZA TA SAKE YI WA PDP BARNA?

*Bisa dukkan alamu fitowar Atiku dan takarar jam’iyyar PDP ta girgiza jam’iyyar APC da magoya bayan ta. A kullum cewa su ke yi mummunan kaye za a yi wa Atiku a zabe, amma kuma a gefe daya APC da magoya bayan ta, ba su da wani aiki sai kamfen na yaki da Atiku a soshiyal midiya da sauran kafafe.

*Zai yi wahala jam’iyyar APC ta samu irin gagarimin goyon bayan da ta samu a fadin kasar nan kamar yadda ta samu a zaben 2015. Shekaru kusan hudu bayan APC ta hau mulki, jam’iyyar ta hadu da matsaloli, cikas, rikice-rikice da kuma rigingimun zaben shugabannin jam’iyya na kananan hukumomi, jihohi da tarayya, wadanda aka hakikance an tafka son kai sosai. Wannan ya janyo wa jam’iyyar cikas.

*Ficewar-farin-dango da aka rika yi a cikin APC ana komawa PDP da sauran jam’iyyu, musamman PDP a Majalisar Tarayya, ya haifar wa APC koma baya matuka. Da yawan sanatoci da mambobin tarayya sun fice, wasu sunn koma PDP jam’iyyar su ta asal, wasu kuma sun shiga wasu jam’iyyu.

*Zarge-zargen zaben-fidda-gwani a tsakanin APC ya karya darajar jam’iyyar. Da dama wadanda aka yi wa ba daidai ba, ba za su maida hankali su da magoya bayan su su yi wa jam’iyya kamfen ko su zabi APC ba.

*Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshimhole na ta gaganiyar fitar da kan sa daga zargin karbar makudan kudaden da ya yi sanadiyyar dagulawa da baddala zabukan fidda-gwani na APC a fadin kasar nan.

*Har yanzu akwai gwamnoni da dama wadanda zaben-fidda-gwani bai musu dadi ba, kuma sun a kan rikici da shugaban na jam’iyyar APC.

*Akwai rigingimu da shari’u masu dimbin yawa kwance a kotu, wadanda hasalallun jam’iyyar APC suka kai kara, tun bayan kammala zaben fidda-gwani. Jihar Rivers da kuma Imo na daga cikin inda rigingimu suka fi tsamari a kotu.

*Tuni dama INEC ta hana APC shiga zaben 2019 a jihar Zamfara, saboda rigingimun da suka tirnike a jihar har zaben fidda-gwani ya gagara a kan lokaci.

*Tulin wadanda suka goya wa Buhari baya a zaben 2019 sun dawo daga rakiyar sa ko rakiyar jam’iyyar sa. Da yawan su sun zuba ido a yanzu, wasu kuma sun sauya sheka.

*Shi kan sa kishin ‘Buhariyya’ din da ake yi, bai kai zafin na 2015 ba. Da dama wadanda suka yi Buhariyya bakin rai bakin fama a baya, yanzu sun watsar da akidar.

*Matsalolin da wasu gwamnoni musamman a Arewa suka haifar wa mulkin Buhari, zai bai wa APC cikas a zaben shugaban kasa.

*An bada kofa ‘yan takara da dama sun kashe kudade sun sayi fam na takara, kuma sunn kashe makudan kudade wajen kamfen na zaben fidda-gwani, amma daga baya an yi musu magudi, wasu kuma an maye gurbin su da wadanda ko ma kamfen ba su fita sun yi ba.

MATSALAR SALON MULKIN BUHARI

*Irin yadda Buhari ke tafiyar da mulkin sa, bai yi daidai da yadda jama’a suka yi tunanin zai yi ba idan yah au mulki. Akwai da dama masu ganin cewa tafiyar mulkin Buhari a karkace ta ke, kuma a daburce.

*YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA da mulkin Buharin ke tutiya da shi, ya na samun cikas ko kuma kakkausar suka daga jam’iyyar adawa da kuma masu sharhin al’amurran yau da kullum. Ana ganin bi-ta-da-kulli ya fi yawa a yaki da cin hanci.

*An fi karkata da maida hankali wajen takura masu adawa a batun yaki da cin hanci, a gefe guda kuma an kyale na jikin gwamnatin Buhari. Rotimi Amaechi, Adam Oshimhole, Bachir Lawan, tsoffin jami’an NIA, SSS, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Babachir Lawal duk akwai alamomin tambaya a kan su.

*Kusan shekara hudu kenan Buhari na yaki da cin hanci da rashawa, amma tsoffin gwamnoni biyu kadai ne aka daure, wato Jolly Nyame da Joshua Dariye. Su din ma ba gwamnatin Buhari ce ta gurfanar da su a kotu ba. Tsohuwar shari’a ce da ta gada.

*Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Godswill Akpabio, wanda EFCC ke neman naira bilyan 117 a hannun sa, a kwanan baya Shugaba Buhari ya yi masa kyakkayawar karba zuwa APC, a daidai lokacin da ake ta tafka shari’ar wasu ‘yan PDP da ake tuhuma da wawurar kudaden da wasun ma ba su kai naira bilyan 1 ba.

*ASUSUN BAI DAYA (TSA) da Gwamnatin Buhari ta shigo da shi, bai hana satar bilyoyin kudade a karkashin mulkin Buhari ba. A kullum ana buga labaran harkalla, cuwa-cuwa da karkatar da bilyoyin kudade da jami’an gwamnatin Buhari ke yi. Fallasa Gwamna Ganduje, kama wasu ministocin Buhari da takardun jabu, kama shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai, Ishaq Kawu da wuru-wurun naira bilyan 2.5 ba karamin cikas ba ne ga gwamnatin Buhari.

*MATSALAR TSARO sai kara munana ta ke yi a Arewacin kasar nan. Duk da cewa Boko Haram sun daina fantsama sun a kai hare-hare a sauran jihohin Arewa, har yau a Jihar Barno sai kara karfi suke yi. Haka kuma sai hare-hare suke kara kaimin kaiwa a garuruwa, kauyuka da kuma gadan-gadan a kan sansanin sojoji. Babu alamar cewa za a iya kakkabe su nan da ‘yan shekaru kadan masu zuwa.

*GARKUWA DA MUTANE a jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da wasu garuruwa ya yi munin da kusan a kowace rana ana ganin aka sace mutane 40 ko ma fiye, musamman a tsakanin yankin Birnin Gwari da jihar Zamfara.

*JA-IN-JA KAN KARIN ALBASHI da ake ta yi domin ganin an kai mafi kankantar albashi ya koma naira 30,000, shi ma babbar matsala ce, domin har ma’aikata sun fara barazanar cewa ko a kara musu ko kuma su yi gaba da Buhari a zaben 2019.

*’Yan Arewa da daman a korafin rashin aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma a jihohin Arewa, musamman a Sokoto, Zamfara, Katsina, Jigawa da Kano inda Buhari ya samu kuri’u masu tarin yawa.

*TATTALIN ARZKIN KASAR NAN da ake cewa ya na farfadowa, cike ya ke da sarkakiya, kasancewa kusan yanzu albashin ma’aikata ne kadai gwamnati ke iya biya da kudaden ribar man fetur da ake rabawa a duk karshen wata. Sauran manyan ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa na kasafin kudade, duk da kudin bashi da lamuni daga kasashen waje ake gudanar da ayyukan.

*FADUWAR DARAJAR NAIRA har yau ta ki sauka ko da kasa da naira 300 a madadin Dalar Amurka daya. Naira daya ta haura fam 400 na Ingila, kuma ta na daidai da Dalar Amurka 360. A kan wannan lissafin ne ake ta ciwo wa Najeriya bashin da babu yadda za a yi kasashen da ke bayar da bashin su yarda darajar Dala, Fam na Ingila da Yuro su karye har naira ta yi daraja.

*JUMA’AR BUHARI TA FARA DAGA LARABA: A kullum Buhari na shan alwashin cewa gwamnatin sa ba za ta yi katsalandan a al’amurran zaben 2019 ba. Da dama sun gamsu da kalaman sa. Da yawa kuma ba su gansu ba, saboda sun auna sun ga yadda aka tafka magudi a zaben shugabannin APC na kananan hukumomi da jihohi. Buhari bai yi komai ba, sai dai cewa ya yi wadanda aka kayar su hakura.

Haka ta faru a zabukan-fidda-gwanin APC a kasa baki daya, zargin tafka magudi ya farraka jam’iyyar APC matuka. A kullum sai rigingimu ke kara kunno kai, bayan kuma wasu na kotu a gurfane. Bayan kammala zaben sai Buhari ya ce wadanda aka yi wa rashin adalci su hakura, ko kuma idan idan abin ya yi maka ciwo, ka tafi kotu mana. Wannan kalami na sa ya bakanta wa da dama rai.

*ZABUKAN EKITI DA OSUN an samo ‘yan matsaloli ta yadda har ita kan ta INEC ta koka da yadda jami’an tsaro suka rika cin zarafin masu kada kuri’a daga bangaren masu adawa da kuma ‘yan jarida. Har yau gwamnatin Buhari ba ta yi komai a kai ba.

*ATIKU: KADA MAJE BA YANKA BA

A can baya Atiku Abubakar ya sha fitowa takara, amma dai a wannan karo na hudu ne ake ganin zai fi yin takarar bakin rai bakin fama. Ko a ce sai inda mai ya kare, ko sai inda karfi ya kare, ko kuma sai inda kudi ya kare. Ba APC ko Buhari ko kuma kowane dan Najeriya ba, duk diniyar da ke bibiyar siyasar Najeriya ma an san a wannan karon Atiku da gaske ya ke yi. Idan ya yi nasara, to PDP ta sake karbe mulki kenan. Idan kuma ya sha kasa, to an yi masa kayen-bankwana-da-siyasa kenan.

*Atiku ya na da goyon bayan kusan sauran ‘yan takarar da ya kayar a zaben fidda-gwani. Wasun su da dama ma su na cikin tawagar kamfen din sa da a a fara kaddamarwa ranar Litinin ta gobe.

*Bakin fentin da PDP ta yi wanka da shi a lokacin gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan, musamman zargin kwashe kudade aka yi kamfen da su a 2015, har yanzu bai gama kankaruwa daga fatar jikin jam’iyyar ba.

*Da dama manyan jam’iyyar wadanda suka taka rawa a lokacin gwamnatin Jonathan wasu ba su kasar, wasu kuma sun yi shiru ba su magana.

*Bisa dukkan alamu har yau Atiku bai dauki darasi ba daga zabukan da ya tana fitowa takara a baya. Gaba daya harkokin kamfen din Atiku sun fi karkata ne a hannun ‘yan kudancin kasar nan. Tafiyar kamfen din Atiku da yada manufofin sa, ba ta cika bayar da muhimmanci a bangaren Arewacin kasar nan ba, musamman ma cikin Hausawa ko kuma bai wa harshen Hausa muhimmanci, a yankin da Buhari ya fi magoya baya.

*ATIKU: KAI KADAI GAYYA: Kusan a iya cewa Atiku Abubakar ne babbar gayya a cikin jam’iyyar PDP. Shi ne uwa kuma shi ne uba, sannan kuma shi ne mai hannu da shinin da kowa zai bai wa murjin zare. Duk wani mai karfi a cikin PDP, to bayan Atiku ya ke.

*MARTANIN ATIKU KAN ZARGE-ZARGEN SA:

“*Matsalar ‘yan Nijeriya ita ce, su a tunanin su, mutum ba zai iya gina kan sa ba, sai ya hada da kudin sata.

“*Abin bacin rai ne a rika amayar da zargin sata a kai na, alhali an kasa fitowa da hujja ko da guda daya wadda ta tabbatar da cewa na wawuri dukiya a lokacin da na ke aiki.

“*Mutane masu dakusassar kwakwalwar rashin tunanin kirkiro dabarun kasuwanci, su a ko yaushe gani su ke yi kowa ma barawo ne kamar su.

“*Idan har Atiku barawo ne saboda kallon irin dimbin kasuwancin da ya ke yi da dukiyar sa, to ina so abokan gabar siyasa ta su fito su shaida wa ‘yan Nijeriya su na su hanyoyin da su ka bi su ka mallaki bimbin dukiyar.

“*Ina kalubalantar duk wani wanda ke da wata hujja ko hujjoji cewa na wawuri dukiyar kasar nan, to kada ya rufa min asiri, ya fito ya tona ni.

“*Idan na zama shugaban kasa, ina da tabbacin cewa zan bai wa kowa mamaki, saboda na yi imani cewa zan yaki da cin hanci da rashawa fiye da yadda kowa ma ya taba yi a baya.

“*Duk da makarkashiya da algungumancin da ake kitsawa don a danganta ni da harkallar William Jefferson a Amurka, an yi shari’ar kuma an kammala tun a 2009, amma ba a kama ni da laifin komai ba.”

KAKA TSARA KAKA

Daga yau dai saura kwanaki 90 a gudanar da zaben shugaban kasa. Abubuwan da za su biyo baya a cikin wadannan kwanaki, sun hada rangadi, hayaniya, kamfen, ambaliyar fastoci da hotuna, tumbatsar marubuta, kalaman adawa a kafafen yada labarai, tuggu da algungumanci da kuma dandazon taro da zugar masu yakin neman zabe.

Tun daga yau Laraba har zuwa ranar 16 Ga Fabrairu, 2019, babu sauran barci mai nauyi a idanun wasu, har sai bayan sun yi nasara, ko kuma bayan sun sha kaye.

Share.

game da Author