TSAFTACACCEN RUWAN: Majalisar Dattijai za ta binciki ayyukan ma’aikatar ruwa

0

A ranar Laraba ne sanata mai wakiltan Kogi ta yamma daga jam’iyyar PDP Dino Melaye ya koka kan rashin samar da tsaftataccen ruwan sha a kasar nan.

Melaye ya kuma zargi ma’aikatar ruwa da yin sama da fadi da kudaden da gwamnati da kungiyoyin bada tallafi ke warewa domin samar da tsaftataccen ruwa a kasar nan.

Ya ce a binciken da ya yi ya gano cewa adadin yawan mutanen dake samun ruwa a kasar nan ya ragu daga kashi 32 bisa 100 zuwa kashi 7 bisa 100 sannan mazaunan karkara kuwa ba a manganar su a wannan harka.

Melaye ya ce abin takaici kuma shine yadda ma’aikatar ke karya da aiyukkan da kungiyoyin bada tallafi kamar su UNICEF, Bankin duniya da sauransu ke yi wajen samar da ruwa musamman a yankunan karkara cewa su ne suka samar da ruwan bayan duk ba haka bane.

Ya ce a dalilin haka yake kira ga majalisar da ta gaggauta bincika aiyukkan da ma’aikata ke yi ganin cewa duk shekara gwamnati na ware kudade a kassafin kudin ta domin samar da ruwa a kasar nan amma har yanzu hakan bai haifar wa kasa da mai ido ba.

Bayan haka sanata mai wakiltan Abia na jami’iyyar PDP Eyinnaya Abaribe ya goyi bayan abin da Melaye ya fada yana mai cewa abin kunya ne a ce yau an wayi gari ababen more rayuwar da aka more su tun a shekarun 1960 basu a wannan karnin na 21 da kowa ya ci gaba.

Ya ce a ra’ayinsa kamata ya yi gwamnati ta samar wa mutanen kasar nan ruwan fanfo amma ba ta yi ta haka rijiyar burtsatse ba.

A karshe majalisar ta amince ta kafa kwamiti da zai bincika menenen ma’aikatar ruwa ke yi da kudaden da gwamnati ke warewa wa da tallafin da ma’aikatar ke samu daga kungiyoyin bada tallafi.

Share.

game da Author