Idan ba a manta ba a ranar Talata ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar da littafinsa da yayi wa lakabi da ‘My Transition Hour’, inda ya bayyana yadda al’amura suka faru a lokacin yana kan kujerar mulkin Najeriya.
Saidai ko awa 24 ba a yi ba da kaddamar da wannan littafin, gwamman jihar Barno, Kashim Shettima yayi wa littafin kaca-kaca inda ya ce tatsuniyoyi ne kawai da karerayi dankare a wannan littafi na Jonathan.
” Na karanta wannan littafi shafi bayan shafi amma kuma abinda na gani ya yi matukar bani mamaki da kunya, ace wai mutum kamar Jonathan ya zauna ya zaro karya, da abinda ba ayi ba yana fadi wa duniya. Duka abinda ya fadi game da Boko Haram labarin gizo da koki ne kawai saboda tun farko ma bai yarda da su ba sannan ko a lokacin da aka dauke matan makarantar Chibok, Jonathan ya fadi kiri-kiri cewa karya ce ba a sace kowa ba zagon kasa ake yi wa gwamnatin sa a lokacin.
A babi na 41 Jonathan ya rubuta cewa wai gwamnatin APC dake mulki a jihar a wancan lokaci ne suka ki taimaka masa domin yayi nasara kan Boko Haram sannan kuma wai shugaban Kasar Amurka Barak Obama shima da gangar yaki taimaka masa a wannan lokaci.
” Idan shi ya manta ni ban manta ba domin a watan Mayun 2014 shi da kansa ya nada kwamiti domin a bi diddigin wannan ayyuka na Boko Haram da ta’addancin da suke yi a kasar nan. Ya nada Janar Ibrahim Sabo. Shi da kan sa ya nada wannan kwamiti kuma ranar 20 ga watan Yuni wannan kwamiti ta mika masa sakamakon binciken da ta yi da kuma baiwa gwamnati shawarwari kan yadda za ta bullo wa abin a kawo karshen sa.
” Amma saboda kin gaskiya, Jonathan boye sakamakon binciken bai bari wani ya gani ba, sai ya buge da cewa ai an kirkiro Boko Haram ne domin ba a kaunar sa ya ci gaba da mulkin Najeriya don shi ba musulmi bane, wato an ga shi kirista ne, ya manta cewa Boko Haram sun fara ayyukan ta’addancin su ne tun a lokacin mulkin marigayi Umaru Musa Ya’adu’a.
“Amma kuma ko a wancan lokaci Jaridar Thisday ta ruwaito cewa ita ta ga sakamakon binciken a boye kuma ta wallafa cewa bincike ne akayi mai zurfi domin har sun rubuta cewa masu binciken sun yaba wa gwamnatin da ke mulki a jihar bisa kokarin da take yi domin ganin abin bai wuce gona da iri ba.
Shettima ya ce surutai ne kawai Jonathan ya tsatssaro amma babu gaskiya a wannan littafi na sa.
Karanta na Turancin a nan: Jonathan’s book elementary, full of fiction – Borno Governor