TAMBAYA: Yaya ake tarbiyyar ‘Ya mace a musulunci, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Yaya ake tarbiyyar ‘Ya mace a musulunci, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdulillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Tambaya mai mahimmanci. Wannan fili namu ba zai isa bada amsar wannan tabaya ba filla-filla. Tarbiyyar ‘Ya mace a
musulunce zai zomuku awannan kafa mai albarka bangare-bangare kuma lokaci bayan lokaci gwargwadon fahimta, muna fatan Allah yabamu dacewa. Amin.

Tarbiyar musulunci itace tarbiyar da aka ginata akan tsarin Al-Kur’ani da Sunna cikin manufofin addinin musulunci.

Tarbiyar musulunci na bukatar fahimtar addini da bin tafarkinsa akcikin rayuwa.

Tarbiyar ‘ya mace bata inganta sai da ingantacciyar tarbiyar da namiji.

Musulunci ya bada falala ga Tarbiyya mata domin sune iyayen al-umma kuma rabin al-umma

YANYOYIN TARBIYAR ‘YA MACCE

1) Tarbiyar ‘ya mace yana farawa ne tun daga zabin miji ko mata.

Mata da miji masu tarbiya su ne za su iya bada ingantacciyar tarbiya ta musulunci.

2) Mata da miji sune taurarin ‘ya’ya, matukar suna kan turbar addini, to ‘ya’yansu ma za su bi sahu.

3) Tsare halal da haram tare da addu’a suma sunada tasiri wajen tarbiyar musulunci.

TARBIYAR ‘YA MACCE: – A Lokacin Yarinta

1) Yawan yin karatun Al-Kurani da sauraren shi, tun daga haihuwar ‘ya mace, hakan zai haifar mata son Al-Kur’ani da karatunsa.

2) Karantar wa da iIlmantar a aikace da karance tare da kiyaye kaidojin addini wajen saya sutura.

3) Tsaida Sallah da sauran ibadu a aikace tare da ita, kuma da nuni gamuhimmancin su, ko falalansu.

4) Koyar da ita kyawawan halaye da kyawawan dabi’u, kamar gaskiya, rikon amana, adalci, da sauransu.

5) A koyamata sanin kimar ‘ya macce, ta salon maga, sanya sutura, tafiya, zama, wasa.

6) A koyamata sanin inda yakamata ta shiga, da inda bai kamata ta shigaba, wanda zata zauna da shi, wanda ba za ta zauna da shiba.

7) A sanyawa kowacce makwancinta da ban.

TARBIYAR ‘YA MACCE: – A Lokacin Da Takai Shekara 10 -15

1) Sanya sutura na shari’ah, da koyar da ita cewa addinin musulunci ya girmamata ta hanyoyi masu yawa.

2) Koyar da ita abubuwan da suka shafeta a matsayinta na budurwa, tare da nunamata hakkokan da suka rataya akanta na addini, zamantakewa da haduran da za ta iya fadawa idan bata kiyayeba.

3) Bata ‘yanci tare da tattaunawa da ita akan abinda ya shafeta domin samar da mafita.

4) Bata kariya daga muyagun kawaye.

5) Koyar da ita tsarin rayuwar ‘ya mace.

Allah ya tsaremana imaninmu da mutuncinmu.

Share.

game da Author