TAMBAYA: Tunda akwai maganar Ahlul-Kitabi a musulunci, ibadar su zai iya kai su Aljannah, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Tunda akwai maganar Ahlul-Kitabi a musulunci, ibadar su zai iya kai su Aljannah, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.

Ahlul Kitabi su ne Yahudawa da Nasara, wato mabiya addinin annabi Musa da littafin Attaura, ko mabiya Annabi Isa da littafin Injila.

An ambace su da Ahlul Kitabi ne sabo da Allah ya saukar musu da littafi da shari’ah. Ibadar su karbabbiya ce, addininsu karbabbene, Al-Jannah itace
sakamakon su matukar sun tsaya kan littafisu da shari’arsu sau da kafa.

Sai dai a yayen da wasu malamai ke fahimtar cewa duk sun yi tarayya a cikin sunan kafirci da sauran mushirikai, wasu kuwa suna fahimtar cewa, Ahlul Kitabi ba su kafirta ba sai an tallata musu musulunci da hujjoji kuma suka ki imani, amma Ahlul Kitabin da musulunci bai kai gare su ba kuma sun rike addinin su, to, lamarin su na ga Allah.

A karshe, lalle Imani da kowane irin Addinin Allah, Musulunci ne ko Nasaranci ne ko Yahudanci ne, kyawawan ayyuka tare da ingantaccen Tauhidi shi ne abinda zai kai bawa zuwa ga tudun tsira cikin rahamar Allah.

Hakika idan Ahlul Kitabi suka yi imanin gaskiya, suka yi aiki na kwarai, Allah zai karbi ibadun su kuma ya sasu a Al-jannah matukar sun tsare Tauhidin su kuma suka yi aiki da shari’ar littafin su. Ayoyi da yawa a Al-Kur’ani suna nuni da haka bisa fahimta ta. Kadan daga cikin ayoyin
sune:
) (1
) (1إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالنَّصَارَى
وَالصَّابِئِينَ مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ
صَالِحاً فَلَهُمْ أَجْرُهُمْ عِنْدَ رَبِّهِمْ وَلا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ
وَلا هُمْ يَحْزَنُونَ) (البقرة:62 (

) (2إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالصَّابِئُونَ
وَالنَّصَارَى مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ
صَالِحاً فَلا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلا هُمْ يَحْزَنُونَ) (المائدة:69)
) (3قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ
بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلَّا نَعْبُدَ إِلَّا اللَّهَ وَلا نُشْرِكَ
بِهِ شَيْئاً وَلا يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضاً أَرْبَاباً مِنْ دُونِ
اللَّهِ فَإِنْ تَوَلَّوْا فَقُولُوا اشْهَدُوا بِأَنَّا مُسْلِمُونَ)
(آل عمران:64 (
) (4إِنَّا أَنْزَلْنَا التَّوْرَاةَ فِيهَا هُدىً وَنُورٌ يَحْكُمُ
بِهَا النَّبِيُّونَ الَّذِينَ أَسْلَمُوا لِلَّذِينَ هَادُوا
وَالرَّبَّانِيُّونَ وَالْأَحْبَارُ بِمَا اسْتُحْفِظُوا مِنْ كِتَابِ
اللَّهِ وَكَانُوا عَلَيْهِ شُهَدَاءَ فَلا تَخْشَوُا النَّاسَ
وَاخْشَوْنِ وَلا تَشْتَرُوا بِآيَاتِي ثَمَناً قَلِيلاً وَمَنْ لَمْ
يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ)
(المائدة:44(
) (5وَلْيَحْكُمْ أَهْلُ الْأِنْجِيلِ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فِيهِ
وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ
الْفَاسِقُونَ) (المائدة:47(

) (6وَلَوْ أَنَّهُمْ أَقَامُوا التَّوْرَاةَ وَالْأِنْجِيلَ وَمَا
أُنْزِلَ إِلَيْهِمْ مِنْ رَبِّهِمْ لَأَكَلُوا مِنْ فَوْقِهِمْ وَمِنْ
تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ مِنْهُمْ أُمَّةٌ مُقْتَصِدَةٌ وَكَثِيرٌ مِنْهُمْ
سَاءَ مَا يَعْمَلُونَ) (المائدة:66(
) (7وَأَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ مُصَدِّقاً لِمَا
بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ الْكِتَابِ وَمُهَيْمِناً عَلَيْهِ فَاحْكُمْ
بَيْنَهُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ وَلا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ عَمَّا
جَاءَكَ مِنَ الْحَقِّ لِكُلٍّ جَعَلْنَا مِنْكُمْ شِرْعَةً وَمِنْهَاجاً
وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَلَكِنْ
لِيَبْلُوَكُمْ فِي مَا آتَاكُمْ فَاسْتَبِقُوا الْخَيْرَاتِ إِلَى
اللَّهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعاً فَيُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ فِيهِ
تَخْتَلِفُونَ) (المائدة:48(

Allah she ne mafi sani .

Share.

game da Author