Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP Isa Ashiru ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai takardun kammala karatun sa da ya mika wa hukumar zabe akwai tsugudidi a ciki.
Ashiru ya bayyana cewa takardun da ya mika wa hukumar zabe sahihai ne garau tas babu garwaye a cikin su.
A tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES a Abuja, Ashiru ya karyata cewa da ake yi wai ya saka hannu a yarjejeniya a tsakanin sa da shugabannin yankin Kudancin Kaduna cewa wai zai ji da su matuka da kuma yi musa alkawura da dama idan har ya lashe zaben 2019.
Ya kuma yi magana game da dabarun da zai yi amfani dasu wajen kada gwamna mai ci Nasir El-Rufai a zabe mai zuwa.
PT: Wani dan jam’iyyar PDP da ya ce ya janye maka a lokacin zaben fidda gwani bisa wani alkawurra da kuka yi da yanzu haka ka yi watsi da wannan shiri na ku da haka ya sa ya fice daga jam’iyyar PDP, Ko za ka iya gaya mana wani irin alkawurra kuka yi a tsakanin ku?
Ashiru: Babu wani alkawari da muka yi da wani dan takara a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.
Ni ma a sama naji wannan zance. Ban sani ba ko ya sanar muku irin alkawarin da muka yi da shi. Amma a sani na ban san da wani yarjejeniya da muka yi da shi ba.
Shi wannan dan takara aminin sanata Ahmed Makarfi ne kuma shi Sanata Makarfi ya kira mu muka tattaunawa tare da shi. A nan ne ya amince ya janye daga takarar. Amma babu maganar wai akwai wani shiri da muka yi da shi kan wani abu da har na saka hannu a takarda ko kuma na ki saka hannu.
Sannan muka tattauna yadda zamu hada kai dukka don mu ciyar da Kaduna gaba idan muka yi nasara a zaben.
Amma ya na da ‘yan cin fadin abinda ya ga dama. Mu 11 ne muka fito takara sannan babu yadda za ace wai na tsame mutum daya tilo na yi wani alkawari da shi ba tare da jam’iyya ta san me nene nake ciki ba.
PT: Kana da masaniyar cewa ana zargin ka da mika takardun boge ga hukumar zabe musamman sakamakon jarabawar ka na kammala makarantar sakandare wato WAEC, Sani Bello da ya fice daga jam’iyyar shima ya ce bai gamsu da takardun ka ba, me za ka ce akai?
Ashiru: Wannan korafi ne da bashi da madafa. Na yi makaranta na sumul Lumui kuma takardun makaranta na duk lafiyayyu ne babu na karya a cikin su. Wadanda na mika wa hukumar zabe lafiyan su lau. Na yi sakandare na a Kufaina, sannan na tafi Katsina na yi Diploma shekara uku, saboda sai da nayi shekara daya na sharan fage tukunna. Bayan nan na yi HND dina a Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Kaduna, sannan na yi bautar kasa a jihar Barno sannan na dawo Kadpoly na yi PGD sannan na tafi jami’ar Bayero in da na yi karatun digirin digir-gir, wato Master’s.
Na yi aiki da gwamnatin jihar Kaduna sannan na yi ritaya a 1997. Yanzu haka ni ina karban fansho.
PT: Idan ka yi nasara a zabe, me za ka yi wa mutanen Kaduna?
Ashiru: Na farko dai za mu duba yadda za mu dawo da cikakken zaman lafiya ne a jihar Kaduna, inda kowa zai samu natsuwa da kwanciyar hankali da cudanya a tsakanin mu. Hadin kai da zaman lafiya shine abin da za mu fi maida hankali a kai. Sannan mu duba yadda za mu gyara aikin gwamnati a jihar Kaduna, domin gwamna mai ci ya yi kaca-kaca da aikin gwamnati a jihar Kaduna. A da wasu daga wasu jihohin kan zo Kaduna domin koyan yadda ake gudanar da aikin gwamnati amma sai gashi yanzu komai ya tabarbare.
PT: A baya ka sauya sheka daga PDP zuwa APC sannan kuma ba da dadewa ba ka sake komawa PDP din, me ya sa ka dawo PDP kuma?
Ashiru: Dama can muzguna mana akayi a Jam’iyyar sai muka ga gara mu fice daga jam’iyyar mu koma inda ba za mu sami matsala ba. Muka komo APC muka hada kai da sauran ‘Yan jam’iyyar muka kada gwamnati mai ci a wancan lokaci. Bayan haka sai ita kanta APC din ta zama jam’iyyar mai gida da yaron gida. Aka fara Isa da nuna iko sannan akayi watsi da mu kuma aka maida jam’iyyar na shafaffu da mai duk da gudunmuwar da muka yi wa jam’iyyar. Daga nan muka kafa APC Akida, wani bangaren jam’iyyar domin mu ja wa jam’iyyar kunne ko ta dawo hanyar gaskiya amma ina. Daga nan ne muka kwashe kayn mu muka fice daga jam’iyyar zuwa muka dawo PDP.
PT: Me za kace game da zaben musulma da El-Rufai yayi a matsayin mataimakiyar sa?
Ashiru: Ay yayi haka ne don siyasa. Amma babu dalilin yin haka. Allah ya riga ya hada mu a jiha daya da mutanen yankin Kudancin Kaduna, dole ne muzauna tare da juna ta yadda za a ba kowa hakkin sa
Abin da ya kamata ayi shi yafi dacewa ayi amma ba son kai da ra’ayin rikau ba. Yana ganin idan yayi haka ne zai ci zabe.
PT: Da gaske ne wai ka saka hannu a wani yarjejeniya da shugabannin SOKAPU cewa za ka nada mutane kudancin Kaduna manya manyan mukamai a Kaduna idan ka zama gwamna da yi musu hidima ta musamman kafin suka mara maka baya a zaben fidda gwani na PDP?
Ashiru: Wannan maganar kanzon kurege ne. Ban san shi ba kuma ni dai ba da ni aka yi ba. Abin da na sani anyi da ni shine mun gana da wasu daga cikin shugabannin su kuma mun tattauna bisa irin ayyukan da zamu yi a jihar. Amma babu wani yarjejeniya da muka saka wa hannu ko wani alkawurra da muka dauka da ake ta yayadawa wai mu yi. Za mu riki kowa a Kaduna da zuciya daya sanan za mu yi aiki tukuru don raya jihar mu da mutane jihar.
PT: Kana ganin za ka iya kada El-Rufai a zaben 2019?
Ashiru: Sanin gaibu sai Allah, tabbas Allah ne kadai yasan gobe. Amma idan El-Rufai zai iya zama gwamna a Kaduna, nima zan iya zama gwamna a Kaduna. Amma mutanen Kaduna ba za su manta irin jagwalgwalon da Nasir El-Rufai ya yi a jihar ba. Muna da yakinin InshaAllah nasara ce ke jiran a gaba.