Takarar Atiku ce za ta tabbatar da imanin masoyan Buhari a 2019, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Allah Ubangiji ya kaimu zaben 2019, cikin lafiya, imani, nasibi da rufin assiri. Muna fatan ganin alheri. Babu shakka siyasa ta fara daukar zafi, ‘yan Arewa guda biyu sun samu damar tsayawa takarar shugabancin kasar Najeriya. Kuma abun sha’awa shine, duk fulani ne jinsin Mujaddadi Shehu Usman Danfodio (Rahimahullah). Babu shakka kallo ya koma sama, za a fafata tsakanin attajiri da mai gaskiya kamar yadda kowa yayi kaurin suna a cikin su.

Gaskiyar lamari za a buga siyasa a idon duk wanda Allah ya raya, za a kuma iya samun siyasar kudi, Anti-party, da rushewar aKida tsakanin magoya bayan ko wane bangare.

Duba da yanayin da talakawa suke ciki na rashin walwala dole za a samu rushewar imanin siyasa wasu masu rauni saboda Atiku Abubakar zai kashe ko nawa ne don ya cika burinsa a Najeriya.

Misali, kowa ya ga abunda ya faru a Fatakol, yadda aka dinga ruwan dala don ita kanta jarida cewa tayi “Ana ruwan dala a Fatakol” Kuma abunda ya faru a zaben fidda gwani na PDP ya nuna cewa sai abunda aka gani a babban zabe saboda zaben fidda gwani kamar sharar fage ne na zuwa babban zabe.

Lallai masoya Buhari sai sun yi da gaske don a nan gaba ne kawai za a tabbatar da imaninsu, kowa ya ga abunda ya faru da makotansu ‘yan Kwankwasiyya a wajen zaben fidda gwani. Sai da aka samu wasu daga cikinsu sun zama bakin ganga.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Annabi (SAW) yace, dukiya fitina ce daga cikin fitinonin da ya bari a doron kasa. Shiyasa muke bawa kowa shawara ya nutsu, misali, idan an lasa muku zuma kun sha kafin zabe, menene matsayinku bayan kun yi zaben an shiga office? Wahala ce amsa kawai, ku dawo hayyacinku ku yi zabe don ci gaban Najeriya, na fada a wata jarida cewa, zaben cikin jam’iya baya tabbatar da ingancin ‘dan takara dari bisa dari tunda a kasashe irin namu an raina wakilcin jama’a. Yakamata hukumar zabe ta dinga kwace duk wani zabe da aka sayar da kuri’a idan kuma ba haka ba, zai wuya a samu canjin gaske.

Professor Jega yace, babu abun da za kayi ka bayyana rashawa karara kamar magudin zabe. Kowa ya san cewa a siyasa zabe shine asalin kowacce gwamnati. Tabbas duk gwaunatin da ta ginu ta hanyar magudin zabe komai ma zata iya yi, kuma siyar da kuri’a babban kalubale ne ga talaka.

Talakawa kada ku manta fa, idan kuka siyar da kuri’arku baku da bakin da zaku tuhimi gwamnati da ta siye kuri’unku don bata yi muku aiki ba tunda kudi ta baku ku ka za6eta. Kai ka taba ganin mutumin da ya karbi cin hanci yana fada da wanda ya bashi? Sai dai idan Allah ne yaso ta tona assirinsu.

Allah yasa mu ga Alheri.

Share.

game da Author