Sojoji 23 kadai Boko Haram suka kasha a harin Metele – Buratai

0

Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa gaba daya sojoji 23 ne kacal Boko Haram suka kashe a harin da suka kai wa sojoji a sansanin Metele.

Buratai ya ce harin da aka kai wa sojojin sansanin Bataliya ta 157, an kuma jikkata sojoji 31.

Kafafen yada labarai na ciki da wajen Najeriya, ciki kuwa har da Reuters, sun nuna cewa an kashe sojoji sama 100 a harin.

Wani soja da ya sha da kyar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kashe abokan aikin sa sama da 70.

Sama da sati daya kenan sojoji ba su fitar da adadin wadanda suka mutu a harin ba, sai jiya Laraba da Buratai ya yi jawabi.

Ya ce wadanda suka ci ciwon duk an rarraba su a cikin asibitoci daban daban a fadin jihar Barno.

Daga nan ya yi ta’aziya ga iyalan mamata da kuma juyayin alhini ga iyalan wadanda aka raunata.

Share.

game da Author