Wani mai gabatar da shaida ya bayyana wa kotu musabbabin kisan da ake zargin Maryam Sanda ta yi wa mijin ta, Bilyaminu Haliru.
Jiya Laraba ne mai bada shaida, fursekito kuma lauya Fidelis Ogbebe, ya gabatar da wani mai bada shaida, mai suna Umar Muhammed, a Kotun Tarayya, Abuja, da ke Maitama, inda ake gudanar da sauraren karar.
Umar, wanda direban mahaifin mamacin da aka kashe ne, ya bayyana cewa:
“ A ranar da aka yi kisan, ina gida kwance, sai na ji kiran waya daga daya daga cikinn abokan aiki na cewa Bilyaminu ya rasu.’’
“Ina jin wannan kiran, sai na fita na garzaya gidan baban Bilyaminu da ke Lamba 1, titin Cassandra, cikin Maitama. Yayin da na shiga gidan, ban samu kowa ba. Da na kira waya, sai aka ce min su na ofishin ‘yan sanda na Maitama.
“ Da na same su a can, sai muka garzaya asibitin Maitama Genaral Hospital, inda aka damka mana gawar sa. Mun dauki gawar Bilyaminu zuwa Babban Masallacin Abuja, domin a yi masa sallah.
“Da ido na na ga na raunuka a jikin sa, daya a wuyan sa, daya a cinyar sa, wani kuma a kan kirjin sa. Sannan kuma na karshen a kan hannun sa na dama. Amma an daura bandeji a kan raunin kan cinyar sa da na kan hannun sa na dama. Ni ne ma na yi wa gawar sa wanka.
Da lauyan wadda ake kara ya mike tsaye, ya tambayi Umar cewa shin ko ya na da masaniyar cewa a musulunce sai dan uwan mamaci ne ko kuma wani kwararren da aikin sa kenan, zai yi masa wanka?
Umar Muhammad ya ce ya sani.
” Shin ka na sane da cewa a musulunce idan za ka yi wa gawar mamaci wanka, sai ka, sai ka rufe ta da daga ruwan ciki har zuwa guyawu?
A nan ma Umar ya ce kwarai ya sani.
Mai gabatar da shaida, sun shaida wa lauya Hussein Musa cewa bai san abin da ya haddasa masa jin raunukan a jikin sa ba.
Mai Shari’a Yusuf Halilu ya dage shari’sar zuwa ranar 3 Ga Disamba, ranar da za a kara gabatar wa wasu shaidu mutum biyu.
Discussion about this post