Sarkin Argungu Sumaila Meira ya bayyana cewa daga yanzu duk sarakunan gargajiya da shugabanin addinai dake Arewacin Najeriya za su hada hannu da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko (NPHCDA) domin ganin an samu nasara a ayyukan yin allurar rigakafi.
Meira ya fadi haka ne a taron da NPHCDA ta shirya domin hada hannu da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai a yankin arewa domin inganta yin allurar rigakafi da aka yi a Abuja ranar Litini.
A dalilin haka ya yi kira ga duk sarakunan gargajiya da shugabanin addinai da su ci gaba da yi wa mutanen su huduba game da ingancin yin rigakafi musamman ga ‘ya’yan su.
Bayan haka shugaban NPHCDA Faisal Shu’ab ya jinjina wa sarakuna bisa wannan hadin kai da suke basu.
Shu’aib ya ka ra da cewa wannan hadin kai zai taimaka wajen ganin anyi wa yara miliyan 4.3 allurar rigakafi musamman wadanda basu yi ba bisa wasu dalilai.