Hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) ta yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar nan da su zage damtse wajen ganin sun kare mutanen su daga kamuwa da cutar sankarau.
Shi dai Sankarau ya kan bullo ne a watanni Nuwamba zuwa Afrilu da idan ba a dau masa mataki da wuri ba akan rasa rayuka da dama.
” Zama da shiri mataki ne da za ta taimaka wajen hana illar da wannan cutar ke yi.
Hukumar ta ce a shekarar 2016 da 2017 cutar ta bullo a jihohi 24 a kasar nan, mutane 14,513 sun kamu da cutar sannan 1,166 sun rasa rayukan su.
” Cutar ta fi yin barna a jihar Zamfara, Skototo da Katsina a bara a dalilin rashin alluran rigakafin sutar.
” Tsakanin bana da badi kasar na da isassun magugunan allurar rigakafi amma duk da haka kamata ya yi gwamnatocin jihohi musamman wadanda suka fi kamuwa da cutar su zama a cikin shiri.
Bayan haka shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na kasa Faisal Shu’aib ya bayyana cewa hukumar za ta hada hannu da gwamnatocin jihohi don ganin an dakile yaduwar cutar.
” Za mu bi duk kananan hukumomin kasar nan domin yi wa mutane allurar wannan cuta.
A karshe Shu’aib ya kuma yi kira ga mutane da su guji yawan cinkoso wuri da, su kuma gaggauta zuwa asibitiidan ba a jin dadi.
Ya kuma yi kira ga malaman kiwon lafiya da su rika yi wa mutane gwaji domin gano cuta kafin su bada magani.
Discussion about this post