Sanata Marafa, shugaban Karamar Hukumar Zurmi sun biya miliyan 11 aka saki tagwaye a Zamfara

0

Kamar yadda masu garkuwa suka bukaci a biya su naira miliyan 15 kafin su saki wasu tagwaye da suka sace a garin Dauran jihar Zamfara, sanata Kabiru Marafa da shugaban hukumar karamar hukumar Zurmi Awwal Moriki ne suka biya naira miliyan 11 kafin aka saki wadannan ‘yan mata.

Masu garkuwan sun bukaci sai an biya su naira miliyan 15 kafin su saki wadannan tagwaye da suka sace a daidai suna raba katin auren su a garin Dauran.

Iyayen wadannan tagwaye mata sun yi ta rokon al’umma da su taimaka koda karo karo ne a ceci rayukan ya’yan su domin su basu da irin wadannan kudade da masu garkuwan suka nemi sai an biya su.

A kwanakin baya daya da ga cikin su ta aiko da sakon murya tana cewa a gaban su an yi ta yi wadanda ba su iya biyan kudin fansa ba yankan rago.

A haka ne fa sanata Kabiru Marafa, cikin tausayi ya aika wa iyayen wadanan mata naira miliyan shida gudunmuwa domin a hada da abin da aka samu wajen jama’a mai taro mai sisi domin ceto rayukan wadannan mata amare.

Shima shugaban karamar hukumar Zurmi Awwal Moriki ya bada tasa gudunmuwar naira miliyan 5.

Da PREMIUM TIMES ta nemi ji daga rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya ce har yanzu ba su same cikakken bayanai a kai ba. Sai dai kuma jaridar Daily Nigerian ta wallafa a shafinta cewa ita har ma tayi magana da wadannan tagwaye bayan an sako su.

Share.

game da Author