Tsohon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara a Fannin Tsaro, Sambo Dasuki, ya rubuta wa kotu wasikar sanar da ita cewa shi fa ya yanke shawarar cewa ba zai sake bayyana a kotun ba har sai Gwamnatin Tarayya ta bi umarnin kotu, ta bayar da belin sa.
Dasuki na fuskantar tuhuma a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, dangane da zargin mallakar makamai a gidan sa da kuma sauran tuhume-tuhume.
Sai dai kuma kotuna daban-daban sun sha bayar da belin sa ba sau daya ba, amma gwamnatin Najeriya ta ki sakin sa, duk kuwa da cika sharuddan beli da Dasuki ya yi.
Wasikar wadda Sambo Dasuki ya aika wa kotu a ranar Litinin 12 Ga Nuwamba, ya rubuta a cikin ta cewa: “Ba ni ba sake zuwa kotu zaman sauraren tuhumar da ake yi mini, tunda ofishin SSS, wanda ejan ne na gwamnatin tarayya shi ma ya bijire wa umarnin kotuna daban-daban, ya ki bada beli na. To ni ma na bijire wa kotun, ba zan sake zuwa kotu ba.”
Sai dai kuma lauya mai gabatar da kara, Dipo Okpeseyi, ya umarci kotu ta ci gaba da shari’ar Dasuki ko da ya ki bayyana a kotu.
Okpeseyin ya ce wasikar Dasuki nuna izgilanci ne ga kotu kuma kokarin kawo tsaiko ne ga shari’ar sa.
Sai dai kuma Mai Shari’a ya ce wa lauya mai gabatar da kara ba zai ci gaba da shari’ar Dasuki ba, har shi mai gabatar da kara ya kawo rubutacciyar rantsuwar shaida cewa da gangan Dasuki ya ki zuwa kotu, don ya kawo wa shari’a cikas.
Mai shari’a ya sake buga misali da hukuncin da ya zartas a baya cikin watan Afrilu da Yuli, cewa:
“Na taba yanke hukunci a cikin watan Afrilu, 10 Ga wata cewa duk ranar da wanda ake tuhuma din ya ki zuwa kotu kamar yadda ya taba yi a baya, to mai gabatar da kara ya je ya kawo rubutacciyar takardar rantsuwa daga kotu, ya rantse a rubuce cewa, wanda ake karar da gangan ya ki zuwa, domin kawai ya kawo tsaiko ne ga shari’ar da ake yi masa.” Haka Mai Shari’a Mohammed ya bayyana.
A daya bangaren, mai shari’a ya ki amincewa ya yanke hukunci a kan wasikar da Dasuki ya aiko aka karanta a kotu, maimakon haka, ya bada umarnin masu kare shi su gabatar da wasikar a cikin rakod na bayanan shari’a, domin kotu da hujjoji ta ke amfani tukunna.
Ya dage shari’ar zuwa ranar 19 Ga Nuwamba, domin a jira a ga ko mai gabatar da kara zai je ya kaiwa kotu rubutacciyar rantsuwar cewa da gangan Dasuki ya bijire wa kotu. Daga nan kuma sai a ci gaba da shari’a ko da Dasuki bai halarta ba.
Discussion about this post