RIKICIN KADUNA: Yadda aka kusa kashe ni da ruwan duwatsu -Wata ’yar jarida

0

Editar Labarai ta Muryar Najeriya (VON), mai suna Temitope ta bayyana yadda ta sha duka, sara da makamai da kua ruwan duwatsu, har ta suma a rikicin Kaduna.

A cikin wata doguwar makalar da ta rubuta a shafin ta na Facebook, wanda ta hada da hotunan ta kwance a gadon asibiti a ranar da abin ya faru, a garin Kaduna, a ranar 21 Ga Oktoba, Temitope ta ce ta hau motar haya ne daga Abuja a kan hanyar ta ta zuwa Kano domin halartar wani taron wayar da kai na ‘yan jarida.

“Ni dai ina ta sharar barci a kan hanya mu na tafiya. Da farko wani fasinja ya zungure ni, ya ce min ya kamata ki daina barci, ki tashi ki wartsake. Na dan farka girgigi, amma na ci gaba da barci, saboda ni ban fahimci komai ba a lokacin.

“Bayan an kara tafiya kuma an kai kan by-pass na Kaduna kafin a kai Kawo, sai fasinjan nan ya kara tayar da ni, ya ce ki fa tashi ki wartsake. To daga nan ne fa na lura da cewa gari fa ba lafiya.

“Mu na lafiya mun kusa kai Kawo, sai mu ga ba wata babbar mota ta gitta titi babu damar motoci su wuce, ga kuma matasa an yi cincirindo. Suka zo kuma kewaye motar mu, kowa dauke da makamai, ga kuma duwatsu a hannun su. A na haka sai suka hange ni a cikin motar, nan take sai na ji direban na rokon su ya na cewa “Don Allah ku yi hakuri”, kuma ni kadai ce mace a cikin motar.

Sannan kuma kayan nan da ku ke gani na sanye da su a cikin wannan hoton su ne na ke sanye, amma na daura dankwali a kai na.

“Wadannan matasa kai da ganin su ka san ‘yan iska ne kawai, kamar su goma sha biyar, sai suka fara dukan motar, a daidai bangaren da na ke. Sauran fasinja kuwa suka runtuma a waje suka tsere.

“Ni kuma na yi ta-maza ta bude kofa ta inda matasan nan su ke, na fito, su na duka na, na fita a guje. Su kuma su ka durfafe ni da duka da sara da jifa, amma ban fasa gudu ba.

“Ina ta gudun fitar rai, ko ta ina ruwan duwatsu kawai na ke ji a kai da sauran sassan jiki na suka sauka. Ina ta gudu su na ta bi na da jifa har na kai wurin wata kwatuwar kwata. Na yanke shawarar tsallale ta, ina yunkurawa, sai na afka ciki. Su kuma suka bi ni da jifa. Tun ina jin zafin saurar duwatsu a jiki na, har na suma na fita daga hayyaci na, ban san inda na ke ba. Kawai na raya a raina mutuwa ta zo kawai.

“Matasan nan sun juya sun tafi sun bar ni, saboda a tunanin su na mutu kawai. Ga jama’a a gefe, amma kowa ba yadda zai iya yi da matasan nan.

“A ranar na ga bala’i da ido na, kuma a kai na. Ga ni kwance jage-jage a cikin kwata, ana saukar min ruwan duwatsu, wasu kuma na kai min duka. Karin abin haushin da ido na ya gane min, shi ne daya daga cikin su ya fito da wayar sa ya na daukar bidiyon jifar da ake yi min ina kwance a cikin kwata.

“Bayan lokaci mai tsawo, na farka na gan ni a wani asibiti na musulmi da ke kan by-pass. Jami’an asibitin sun shaida min cewa wani soja ne, kuma ina jin musulmi ne, shi ya kai ni asibitin. Amma da farko suka ce ba za su karbe ni ba, domin a na su tunanin na mutu kawai.

“Sojan nan ya yi ta tankiya da su, har dai a karshe ya ajiye ni a asibitin ya juya ya ce musu su jaraba dai su gani, shi a tunanin sa kamar ina da sauran kwana a gaba.

“A asibitin nan na bayar da lambar iyaye na daga baya kuma ta abokan aiki, inda daga nan fa suka kasa barci har garin Allah ya waye su na buga waya su na tambayar asibitin halin da na ke ciki.

“Ashe matasan nan ba su hakura ba, bayan sun ji labarin wai an dauke ni an kai ni wannan asibitin. Sai suka je asibitin suka nemi a ba su ni su karasa kashe ni. Jami’an asibitin suka kulle ni a wani wuri tare da wata ma’aikaciya, suka ce komai rintsi, komai wahala da takura, kada ta sake ta bude wa kowa kofar, sai fa shugaban asibitin da wasu ma’aikata kawai.”Inji Tamitope.

A karshe dai Temitope ta gode wa Ofishin VON na Tarayya a bisa kulawar da suka nuna mata bayan da aka gano inda ta ke, ta gode wa ma’aikatan VON a Kaduna, kuma ta gode wa Gwamnatin Jihar Kaduna, wadda ta turo Kwamishinan Lafiya da kan sa ya je ya same ta har asibiti.

Ta ce daga baya an maida ta asibitin sojoji, bayan ta dan ji sauki kuma aka maida ta Abuja.

Share.

game da Author