RIKICIN APC: Doka ba ta hana ni zama gwamna don ina auren ’yar gwamna Okorocha ba -Nwosu

0

Dan takarar Gwamnan Jihar Imo a karkashin jam’iyyar APC, Uche Nwosu, ya bayyana a tsarin dokokin fitowa takara, babu inda aka gindaya sharuddan cewa don ya na auren ‘yar Gwamna Rochas Okorocha, to kada ya fito takarar zabe.

Nwosu, wanda ya taba yin kwamishinan kasa da Safiyo na jihar Imo, a yanzu shi ne Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, kuma mai auren ‘yar Gwamna Okorocha.

Fitowar Nwosu takara bisa saurin gindin Gwamna Okorocha, ya jefa APC a jihar cikin rikici, inda shi ma Sanata Hope Uzodinma ke ikirarin shi ne sahihin dan takara.

Nwosu ya kuma karyata cewa Okorocha ya tsaida iyalan sa takara domin ya ci gaba da yin yadda ya ga dama a jihar.

Har ila yau, kokarin tsaida Nwosu takara ta haifar wa Okorocha rikici da Shugaban Jama’iyyar APC na Kasa, Adams Oshimhole.

Da farko INEC ta lika sunan Uzodinma a cikin jerin ‘yan takarar APC na kowace jiha, amma daga baya kuma sai ta cire sunan sa, saboda kowane bangare ya kai kara kotu, ya na neman a soke daya bangaren. Wato rigimar su ta na kotu tukunna.

Ya ce shi ba dan’uwan Okorocha ba ne na jini, sirikin sa dai ne kawai, kuma ba daga karamar hukuma daya suka fito ba.

Nwosu ya kara da cewa yawancin tsare-tsaren birane da aka yi a karkashin wannan gwamnati ta Okorocha, duk shi ne ya kirkiro su.

Share.

game da Author