Kwararru a ma’aikatan kiwon lafiya sun koka kan yadda gwamnatin tarayya ta gagar ware kaso daya daga cikin kasafin kudin 2018 wa fannin kiwon lafiya.
Jami’in cibiyar ‘Development Research and Project Center (dRPC)-PAS’ Emmanuel ya ce fannin kiwon lafiya ta sa ran samun wannan kudi domin zai taimaka wajen inganta aiyukkan asibitocin kasar nan amma sai ga shi hakan bai tabbata ba.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati ta amince ta rika ware kashi daya daga cikin kasafin kudinta na kowani shekara domin inganta fannin kiwon lafiya.
” Hakan zai taimaka wajen inganta kiwon lafiya da mutane musamman mazauna karkara, rage yawan mace-macen yara da mata da inganta amfani da dabarun bada tazarar iyali a kasar nan.
Wani ma’aikacin kiwon lafiya Dale Ogunbayo da yake ganawa da PREMIM TIMES ya bayyana cewa samun kaso daya daga cikin kasafin kudin shekara domin inganta fannin kiwon lafiya na cikin sauran fannonin dokar NHA da har yanzu basu fara aiki ba.
Ogunbayo yace hakan na da nasaba ne da rashin kishin kasa da ‘yan siyasan kasar nan ke da shi da rashin hadin kan ma’aikatun dake karkashin ma’aikatar kiwon lafiya.
” A yanzu haka babu hadin kai a tsakanin ma’aikatun dake karkashin ma’aikatar kiwon lafiya inda wasu hukumomin na ganin cewa bai kamata suna karkashin ministan kiwon lafiya ba.
A dalilin haka Ogunbayo ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukan mataki kan haka.
Discussion about this post