RAHOTON MUSAMMAN: Yadda NNPC ya Shiga Kaka-na-ka-yi

0

Kamfanin Kula da Hada-hadar Mai na Tarayya, NNPC ya shiga cikin tsaka-mai-wuya, ta yadda bashin naira tiriliyan daya ya shake masa wuyan da ba ya iya numfasawa ya gudanar da muhimman ayyuka.

Wasu sahihan takardun bayanai da suka fado a hannun PREMIUM TIMES, sun nuna cewa a yanzu NNPC kokari ya ke yi, ya na kokarin kubuta daga cikin halin-kaka-na-ka-yin da ya fada, watanni sha daya, tun cikin watan Janairu, amma ya kasa kubuta.

Dalla-dallar Yadda NNPC Ya Shiga Kaka-na-ka-yi:

1 – Takardun bayanai sun nuna cewa tsakanin watan Disamba, 2017 zuwa Janairu, 2018, NNPC ba ta da kudin da za ta shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje. Hakan ya sa aka kasa shigo da shi, aka rika kame-kame.

2 – Takardun sun bayyana irin mawuyacin halin da NNPC ta shiga a farkon wannan shekara, cikin bayanan har da kwafen wasikar da Shugaban NNPC Maikanti Baru ya aka wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda mahukuntan NNPC suka nuna damuwar su dangane da yawan man fetur din da suka ce ana sha a Najeriya a kowace rana.

3 – Wasikar da Baru ya rubuta wa Buhari a ranar 19 Ga Janairu, 2018, ta nuna damuwa kan yadda rumbunan ajiyar man fetur na kasar nan ke ta yin kasa a kowace rana, saboda yawan karkatar da man fetur da kuma kimshewa ana boyewa da ake yi a kullum.

*Baru ya shaida wa Buhari cewa fetur din da ake sha a Najeriya ya kai lita milyan 47 a kowace rana – duk kuma da cewa gaskiyar wanda ya kamata a ce ana sha a kullum bai wuce lita milyan 35 ba, idan ma har ya kai din.

4 – Baru ya rubuta a cikin wasikar cewa idan ba a magance matsalar ba, to za a afka cikin mawuyacin halin da ka iya haifar da tada harzoma.

5 – Daga nan sai Baru ya nemi da Gwamnati ta dunbuza wa NNPC makudan kudade domin ta shawo kan matsalar.

6 – Baru ya bai wa Buhari shawara, biyo bayan wata shawara da shi Buhari ya bayar a baya cewa, NNPC a lokacin fa ba ta iyawa ko kuma ba ta da kudaden da za ta iya kwasa ta sayo fetur daga waje.

7 – Maikanti ya shawarci Buhari da a kyale NNPC ta yi canjin kudaden kasashen waje a farashin da ya dace da mafi arhar da za ta iya yin jigilar shigo da fetur daga kasashen waje.

8 – Maikanti ya shaida cewa idan fa ba haka aka yi ba, to NNPC ba ta da kudaden da za ta iya shigo da fetur, har ya wadaci wayan wanda ake bukata a kullum a kasar nan kuma har ta adana wani kason da ta ke tarawa a rumbunan adana man fetur din ta a kasan nan.

9 – Maikanti ya ce tulin bashi ya rigaya ya yi wa NNPC katutu, ya shake mata wuya, ta yadda ba za ta iya yunkurawa ta kara ciwo wani bashi ba, saboda bashin da ke kan kamfanin ya kai naira tiriliyan 1, ya zuwa lissafin karshen shekara da kamfanin ya yi a ranar 31 Ga Disamba, 2016.

10 – Bugu da kari kuma, manyan masu binciken hada-hadar kudade sun shaida wa NNPC cewa ba ta iya biyan bashin da ke wuyanta a daidai ko kuma kafin wa’adin biyan bashin ya cika.

11 – Kudaden da NNPC ke da su ya zuwa 12 Ga Janairu, 2018, cikin cokali ne, ba su wuce naira bilyan 176 ba sai kuma wasu dala milyan 8, wadanda idan aka hada su, ko alama ba za su kai wadatar kudaden da ake bukata a sayo domin a magance matasalar ba.

12 – Bugu da kari, Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi na bin NNPC cikon naira bilyan 406.13, daga kudaden kason ribar mai da ba ta ba su ba a watan Okotba, Nuwamba da Disamba, 2017. Idan ta cire kudaden ta bayar, to dan abin da zai rage a asusun NNPC ba zai wuce naira bilyan 120 ba.

MATSALAR TULIN BASHI KAN BASHI:

Kakakin Yada Labarai na NNPC, Ndu Ughamadu ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa yanzu lalitar kamfanin NNPC na habaka sosai, tun daga lokacin daga lokacin daga lokacin da ta karbi kudi a bisa tsarin ‘biyan-bashin-daddawar-kauye, daga Asusun Tara Kudaden Gas na Najeriya, wato NLNG.

Ya ce tilas ta sa NNPC ta karbi bashin kudaden daga NLNG, saboda Majalisar Tarayya ta umarce da ta bi duk hanyar da za ta iya bi domin ta samu kudaden da za yi amfani da su wajen ganin ta shigo da man fatur daga kasashen waje, yadda zai wadaci kasar nan, har kuma a samu wanda za a iya adanawa, saboda kwana da shirin ko-ta-kwana.

Ya ci gaba da cewa a halin yanzu ana amfani da wannan bashi na dala bilyan 1 daga NLNG ana sayo fetur daga kasashen waje da kudaden.

IDAN BA KIRA ME YA CI GAWAYI

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa idan gaskiya ne ana amfanin da kudaden bashi gada NLNG ana shigo da mai daga kasashen waje, to me ya sa kuma NNPC ba ta iya cika wasu ka’idojin da suka wajaba a kanta?

DALILI: Tsakanin watan Janairu har zuwa Yuli, NNPC ta kasa gabatarwa Asusun Tarayya da ake rabawa a kowane karshen wata gamsasshen bayanin kudaden da aka tara za a raba wa Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi. An Majalisar Gudanarwa ta sha taruwa a Fadar Shugaban Kasa, amma ana tashi ba tare da an raba ko sisi ba, saboda NNPC na ta yin kwan-gaba-kwan-baya.

A watannin Maris, Afrilu da Mayu haka wakilan jihohi 36 da Abuja suka taruwa a Abuja sun a watsewa saboda tarnakin da ya dabaibaye kudaden da NNPC ta ce su kadai za ta iya bai wa Asusun tarayya domin rabawa a karshen kowane wata.

Jula-jular da aka yi a cikin watan Yuli ta fi ta sauran watannin baya zafi, domin an yi ta gudanar da taruka tsakanin NNPC, Ministar Kudade ta lokacin, Kemi Adeosun da hukumar Raba Kudaden Gwamnatin Tarayya, inda aka rika neman mafita.

AN KARKATAR DA KUDADEN

Kwasar dala bilyan 1.05 da aka yi daga NLNG aka ba NNPC ta rika shigo da fetur daga waje, karya doka ce sosai, domin kudaden hakkin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi ne. Wannan ya kara jefa su cikin alakakai matuka.

Share.

game da Author