Wannan wata tattaunawa ce mai zafi da Gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya yi da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, bayan ganawar da gwamnonin APC suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari.
Wakilin PREMIUM TIMES na cikin wadanda suka gana da gwamnan:
Tambaya: Me ya kawo ku ganawa da shugaban kasa, kuma me ku ka tattauna da shi?
Okorocha: Ina gaishe da dukkan ‘yan jarida da ke nan murin, sannan kuma na tsaya tare da ku domin na sanar da ku cewa ba gaskiya ba ne da ake cewa shugaban kasa na goyon bayan wankan-gurmaden da shugaban APC, Adams Oshimhole ke yi wa jam’iyyar APC. Daga abin da na fahimta, shugaban kasa bai taba umartar Oshiomhole ya yi wani abu ko da sau daya da ya karya doka ba. Kuma bai taba cewa ya yi wani abu na rashin adalci a tsakanin APC ba.
Saboda haka Oshiomhole shi kadai ke kidan sa, kuma shi kadai ke rawar sa. Bai taba samun wani goyon baya daga fadar shugaban kasa aka ce ya soke sunan dan takarar da ya yi nasara, ya maye gurbin sa da wanda ya sha kasa ba. Don haka babu ruwan shugaba, harkalla ce kawai ta Oshimhole shi kadai, kankin kan sa.
Sannan kuma na nemi lallai Oshiomhole tilas fa ya rika bin umarnin doka da oda kuma ya rika bin umarnin kotu, a inda duk kotu ta bayar da umarni. Tilas ya daina yi wa kallon takardar umarni daga kotu kamar darajar ta daya da takardar goge majina. Tilas ya tashi ya dinke mummunar barakar da ya haifar a cikin jam’iyya, saboda kowa ya yi tunanin cewa alheri Oshimhole zai kawo wa APC, amma sai ya shigo wa jam’iyyar da akasarin haka.
Tambaya: Yanzu za a iya cewa daurin tsintsiyar APC ya kwance, duk ta tarwatse kenan?
Okorocha: To, APC ba za ta tarwatse ba, muddun dai Muhammadu Buhari ne shugaban Najeriya, kuma ya ci gaba da zama shugaba kuma jigon jam’iyyar. Amma ba za mu ce APC na tsaye a kan kafafuwan shugaban jam’iyya ne, Adams Oshiomhole ba. Sai dai kuma zan iya cewa Oshimhole ya ji wa mambobin jam’iyya da dama mummunan rauni, kuma sun fusata. Tun bayan da ya hau, zuwa lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani, mun rasa kimanin maboya baya milyan biyar, wadanda suka fusata, suka harzuka daga rashin adalcin da Oshiomhole ya gantsara musu.
Tambaya: Ranar Juma’a ce INEC za ta rufe karbar sunayen ‘yan takara. Wane hali jihar Imo ke cike? Shin har yanzu Oshimhole ya na bayan bangaren Hope Uzodimma ne?
Okorocha: Ai ba zai iya goyon bayan Hope Uzodimma ba, saboda Hope dai bai ci zaben fidda gwani ba.
Ta yaya za ka hada wanda ya samu kuri’a 265,000 da kuma wanda ya samu kuri’u 7,000 tal?
Hope bai ci zabe ba, kuma sai ka dora wa jama’a wanda ba su zaba ba, kuma ba za su amince da shi ba? Ya kamata ya yi abin da ke daidai, kamar yadda na sha shawartar sa a baya cewa ya yi abin da ke daidai tun kafin ya kara haddasa wata sabuwar rigimar rabuwar kawuna a cikin APC.
Tambaya: A yau an ce Kwamitin Gudanarwa na Kasa ya mika wa INEC sunan Hope Uzodimma. Mene ne gaskiyar lamarin, kuma me hakan zai haifar a cikin APC?
Okorocha: Ba fa zai iya yin wannan kasassabar ba! Ba na jin NWC za su yi haka, saboda tun da farko dai kwamitin ya tura mutane 13 domin gdanar da zabe, kuma 12 daga cikin su suka saka hannu kan sakamakon zabe, cewa Uche Nwosu ya samu kuri’u 265,000, shi kuma Hope ya samu 7,000 kacal. NWC sun rubuta takarda cewa Uche Nwosu ya yi nasara, har an ba shi takardar shaida. Hukumar ‘yan sanda da INEC duk sun rubuta rahoto cewa Uche Nwosu ne ya ci. Ta yaya kuma za a ce za a bada sunan Hope Uzodimma? Ai ba ma zai yiwu a yi haka din ba.
Tambaya: Jiya kuma jigon APC Bola Tinubu, ya zo nan, ya ce mana Oshimhole mutumin kirki ne, ya iya rike jam’iyya, ya kira hasalallu irin ku su dangana su mara masa baya. Ka na nufin Tinubu bai san wanda ya kamata ya mara wa baya ba kenan?
Okorocha: A gaskiya mai yiwuwa ba a fada wa Tinubu gaskiyar shirmen da Oshimhole ke tafkawa ne kawai. Amma idan da ya san irin kwakyariya da harankazamar da ya ke yi, ba zai fito a gaban jama’a ya ce Oshimhole ya iya tafiyar da shugabanci ba.
Tambaya: Ana jita-jitar cewa za ta koma SDP?
Okorocha: SDP kuma? Ta yaya zan gina gida sannan kuma na fice na bar wa wani ya shiga ya mike kafa? Ina cikin APC, ni na kafa APC, ni na rada mata sunan APC. Don haka jam’iyyar mu ce, kuma ina ciki, tilas sai mun tsaya mun ga ta kara bunkasa.