A farkon wannan makon ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da tambari da kuma taken sabon salon kamfen din san a yakin neman zaben 2019, inda ya rika dukan kirjin cewa ya gina kakkarfan ginshikin zaunar da Najeriya a kan turbar ci gaba. Wannan ya sa shi cewa yanzu kuma za a shiga mataki na gaba na ci gaban kasa, wanda kuma sunan taken na sa kenan, watau ‘Next Level’.
An dai fara kamfen tun a ranar Lahadi da ta gabata, inda aka bude sabon lalen fafata yakin neman zabe tsakanin Buhari da ke kan mulki a karkashin APC da kuma Atiku Abubakar a karkashin jam’iyyar PDP.
Da ya ke Buhari shi ne ke kan mulki, takarar sa na fuskantar matsanancin sharhin masu tankade da rairayar shekarun da ya shafe ya na mulki musamman a batun tattalin arziki da matsala ko kalubalen tsaro.
Farkon abin dubawa shi ne yadda dimbin ‘yan Najeriya ke ta rasa aikin yi a kowace rana. Ga rikicin makiyaya da na manoma wanda ya ci rayukan dubban jama’a cikin shekarun da suka gabata.
Sannan kuma rahotannin cikin gida da na wajen kasar nan, su na nuna cewa wadannan rikice-rikice na kara raba kawunan jama’a da kuma ruruta kabilanci.
Sai dai kuma Najeria ta samu nasara a bangaren yaki da Boko Haram. A baya kusan ‘yan ta’addan sun mamaye yankuna da dama a Arewa maso Gabas kuma dukkan jihohin Arewa har da Abuja su na kai hare-hare a lokacin Jonathan, watau mulkin PDP.
Amma fa har yanzu su na ci gaba da kai hare-hare a Arewa maso Gabas na sunkuru, musamman ma a kwanan nan da suka matsa lambar kai wa sojoji munanan hare-hare.
Har yanzu kuma dubun-dubatar masu gudun hijira bas u koma garuruwa da kauyukan su ba tukunna.
Duk da wannan, Buhari ya jajirce cewa shi fa har yanzu bai kauce hanya ba daga alkawurannan da ya dauka na farfado da tattalin arziki da samar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa ba.
Ya ce idan aka sake zaben sa, to zai kara cicciba Najeriya zuwa mataki na gaba, watau matakin dauwamar da kakkarfa ingantaccen tattalin arzikin kasa.
PREMIUM TIMES ta yi nazarin sabon daftarin kudirorin alkawurran zaben Buhari na zaben 2019. Buhari na so idan aka sake zaben sa ya ci gaba da jaddada wato ajandojin sa biyar kamar yadda nazarin ya nuna.
1. SAMAR DA AYYUKAN YI
Sanarwar da kafar yada labarai da kididdiga mallakar gwamnatin tarayya, ta nuna cewa gwamnatin Buhari ba ta tabuka komai ba wajen samar da ayyukan yi.
Rashin ayyukan yi a Najariya ya shafi sama da mutane milyan 18.8.
Sannan kuma tun cikin 2017 har yau Hukumar Kididdiga ta Kasa ba ta sake bayyana yawan masu aiki ko marasa aikin yi a kasar nan ba. Wannan ya sa ana zargin hukumar da gazawa saboda wasu dalilai na siyasa.
Wannan matsalar rashin aiki yi, ta sa shirin gwamnati na ramta wa wasu manoma kudi. Da kuma tsarin N-Power duk basu yi wani tasiri a idon jama’a ba.
A bangaren samar da aikin yi idan ya sake cin zabe, babu wata hanyar da aka kirkoro da ta bambanta da ta alkawarin 2015, sai dai kawai fadada aikin da aka sha alwashin yi a 2019.
Na farko a yanzu Buhari ya yi alkawarin samar da aiki ga matasa milyan 10 a karkashin N-Power da kuma samar da aiki a fannin sana’o’in hannu har ga matsa milyan 10.
Na biyu akwai alkawarin samar wa milyoyi aikin yi ta hanyar bada lamuni ga manoma milyan daya, inganta Tsarin Kiwon Dabbobi wanda zai samar da aiki ga mutane milyan 1.5. samar da kindirmo, fata, nama, amfanin gona, inganta aikin noma da kuma samar da taraktoci da za su samar wa matasa milyan 5 aikin yi.
Na uku yace zai samar da dala milyan 500 domin kananan masana’antu su samar da aikin yi ga mutane dubu 500. Sannan kuma za a yi wa matasa 20,000 horon sana’o’i.
Na hudu Buhari ya yi alkawarin samar da aiki ta hanyar kirkiro Masana’antu Shiyyoyi da Shiyyoyin Inganta Tallain Arziki na Musamman da sauran su.
Na biyar kuma Buhari ya yin alkawarin kara samar da aikin yi 300,000 ga masu talla da manoma ta hanyar kara yawan daliban da za rika ciyarwa a makarantu daga milyan 9.2 zuwa milyan 15.
2. SAMAR DA ABABEN MORE RAYUWA
A nan Buhari ya sake daukar alkawarin gina hanyoyin na jiragenn kasa, Babbaar Gadar Kogin Neja ta 2, samar da hasken lantarki ga jami’o’i da kasuwanni 300 ta hanyar hasken sola, da inganta hasken lantarki zuwa migawat 12,000 da sauran su.
3. KASUWANCI DA SA’AO’I ma Buhari ya yi alkawarin tallafa wa masu kananan masa’antu da karamin jari na ‘trader moni’, ‘people moni bank’ da sauran hanyoyin samar da sana’o’i a saukake.
Ya ce idan an zabe shi wasu matasa milyan 10 za su samu aikin yi a karkashin wannan tsari, fiye da milyan 2.3 da ya ce sun samu a wannan zangon na sa da ake ciki.
4. Bangaren Kiwon Lafiya da inganta Ilmi Buhari yayi alkawurra da dama, ciki har da alkawarin gyara makarantu 10,000 a kowace shekara.
A bangaren lafiya kuma ya ce za a sama wa masu karamin karfi inshorar kiwon lafiya ta yadda za a rika rage musu kashi 40 cikin na dawainiyar magunguna.
5. JAWO JAMA’A A CIKIN GWAMNATI
Buhari ya yi alkawarin bai wa mata kaso 35 bisa 100 na mukaman da aai raba idan ya sake yin nasara a zaben shugaban kasa a 2019. Zai kara samar wa matasa aiki a cikin gwamnati kuma matasa sabbin kammala jami’a za su rika samun aiki a karkashin ministoci da manyan ma’aikatan gwamnnati na hukumomi.an tsaron da suka kafa a kauyen.