Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta mika goron neman bashin dala bilyan 2.86 domin karasa wasu ayyukan da ke cikin kasafin 2018 da kuma aiwatar wasu muhimman ayyuka.
Ma’aikatar Harkokin Kudade ta bayyana cewa kudaden sun hada da dala bilyan 1.18 wadanda aka yi yarjejeniyar shekara bakwai, sai kuma dala bilyan 1 da aka yi yarjejeniya ta tsawon shekaru 12. Akwai kuma wata dala milyan 750 a karkashin yarjejeniyar shekaru 30.
Za a biya kudin ruwa na kashi 7.625 a karkashin yarjejeniyar shekara bakwai, sai kuma kudin ruwa na kashi 8.75 a karkashin yarjejejiyar shekaru 12. Dala milyan 750 da ke karkashin yarjejeniyar shekaru 30 kuwa, za a biya mata kudin ruwa na kashi 9.25.
Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa duk da fadi-tashin da kasuwar danyen man fetur ke yi a kasuwannin duniya, Najeriya ta yi kokarin cike sharuddan karbar lamuni a cibiyoyin hada-hadar kudade ta duniya domin karasa ayyukan kasafin kudin 2018, a kan farashin da bai kai tsaurin na sauran kasashen Yankin Saharar Afrika ba.
Ta ce za a yi amfani da kudaden domin cike gurbi da gibin da aka samu a kasafin kudi na 2018 da kuma sauran wasu muhimman ayyukan raya kasa da gwamnati ta sa a gaba.
“Bangarorin da za a yi ayyuka da kudaden sun hada da sufuri, lantarki, aikin gona, samar da gidaje, kiwon lafiya, ilmi da kuma sauran tsare-tsaren inganta rayuwar jama’a, wanda a yanzu ake ganin alfanun wanda aka rigaya aka fara yi.”