Babban abin da za ka yi wa abokinka, shine ka zama abokinsa. -Henry D. Thoreau (1817-1862)
Wani abu da har yanzu yake neman ya zamarwa Najeriya kalubale kususan a tsaron cikin gidanta shine, ta kasa rarrabe su waye abokan arziki da kuma abokan tsiya. Domin kuwa sama da shekaru hamsin da samun ‘yancin kai, Amma har yanzu abubuwan da ke gudana sun kasa rarrabe wace kasa ce ya kamata a ci gaba da zumunci na gaskiya, wacce ce kuma ta dace da na bogi?
Wani muhimmin batu da ya ja hankalina dangane da wannan rubutu shine yanda har yanzu matsalar tsaro ke ci gaba da kawowa kasarnan barazana ta zahiri da badini ta fuskoki da dama. Kuma idan har ba ayi da gaske ba, irin wadannan kasashe za su iya yin nasara wajen tarwatsa Najeriya nan da wasu shekaru, duk da cewar ba fata ake yi ba.
A cikin jamhuriyya ta farko, Anthony Enahoro ya taba gabatar da wani kuduri a majalissar tarayya a Lagos, in da ya bukaci firaminista Tafawa Balewa da su yi kokarin daidaita ainahin manufofi da alakar Najeriya da sauran kasashen duniya. Amma sai aka dau haka da muguwar manufa ko rashin kishin kasa, har wasu daga mutanen Arewa suka yi wa abin caaa, a karshe komai ya baje bai je ko ina ba. Kuma gashi a Yanzu abubuwa na ta faruwa marasa dadi ga kasa.
Kasar Benin, Nijer, Chadi, Kamaru su ne kasashe hudu da kasar Faransa ta mulkesu, kuma su ne suka zagaye Najeriya. Wani Abin mamaki, duk kasashe hudu idan za a hadesu, to Najeriya ta fisu a komai. Don haka abu ne mai sauki komai ya iya faruwa, na dangane da wani yunkuri na kawo rashin tsaro a Najeriya daga wadannan kasashe na makota. Wannan batu zai iya bayyanuwa idan aka nazarci matsalar Boko Haram Kawai.
Kasar Saudiyya da Iran suma sun kafa wani dashe mai karfi wanda shima zai iya zama barazana ga zaman lafiyar Najeriya nan da wasu shekaru. Saudiyya na daukar nauyin kungiyar Jama’atul Izalatul bidi’a wa’ika matus-sunnah (JIBWIS) wanda aikinsu kai tsaye shine assasa ayyukan Sunna a Najeriya da kuma makota. Sai kuma kasar Iran da itama ke kula da kungiyar Islamic Movement of Nigeria.
(IMN) ita ma kai tsaye suna aiki ne a karkashin kasa don ganin an yada manufar akidar Shi’a a Najeriya da makota. Idan kuwa har hakane, kun ga an tafi wani yanayi da tsaro da zaman lafiyar Najeriya ya dogara ne da yanda wadancan kasashe uku ke kallon Najeriya.
Ku kalli yanda kasar Syria ta koma filin zubar da jini gami da kisan rai akan kawai akida ta addini da kuma manufa ta tattalin arxiki. Kuma wannan sakaci da suka yi a baya, har Sunni da Shi’a su ka kai matsayin da za su iya yakar juna, to a sannu a hankali mu ma za mu iya shiga hakan. Domin kowa yasan kuma ya sha ganin yanda wadannan kungiyoyin addinan biyu ke ta yawan fareti na jiran ko ta kwana dangane da yamutsi ko hargitsi.
Daga karshe, duk da cewar kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da damar addini gami da yin kungiyar da mutum ya ga dama, to abu ne mai kyau ‘yan majalissu su zauna gami da kungiyoyin masu kishin kasa, su sake nazarin ainahin alakar Najeriya da irin wadannan kasashe da za su iya zamo mana barazana nan gaba.
Kar ku manta, a addinance, sai da Sir Ahmadu Bello ya rasu, bayan su Nzegwu sun kashe su, kana kungiyoyin addinai su Shi’a da Dariku suka fara shigowa. Kowa ya san Jama’atu Nasrul Islam ce kadai ke wakiltar musulman Najeriya. Amma a yau, bayan shekaru da tafiyar su, an wayi gari kungiyoyi sun yi karfin da za su iya fafatawa da sojojin Najeriya da sauransu.
Ya kamata idan har abotar da za mu yi da sauran kasashe za ta haifar mana da matsala ce, to dole mu yi kokarin daidaita kusanci ko nisantar junanmu da su. Kar ku manta, a cikin watanni da suka wuce kasar China take ta rusa masallatai da majami’oi da sunan rage masu tsaurara akidun da su ma za su kawowa kasa matsala a nan gaba. Don haka ya kamata ita ma Najeriya ta yi kallon nutsuwa ta nazarci hakan, don ganin an kawo zaman lafiya mai dorewa.
Domin kuwa da yawa daga masu kawo wa kasa matsala a bangaren addini, ba su ma gama fahimtar addinin ba.