Mata ta kashe mijinta da ‘ya’yan su uku sannan ta burma wa cikinta wuka

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai ta bayyan cewa wata mata ta kashe kanta, mijinta da ‘ya’yan su uku.

Kakakin rundunar Moses Yamu ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa mijin matar mai suna Nicholas Adetsay ma’aikacin karamar hukumar Makurdi ne sannan da shi da ‘ya’yan sa uku sun gamu da ajalinsu ne a ranar Juma’a da yamma

”Mun shiga gidan Adetsay ranar Asabar inda muka iske gawarwakin Adetsay, ‘ya’yansa uku da matar.

Yamu yace makwabta sun bayyana musu cewa gidan Adetsay ya dade da zama filin daga domin babu rana babu dare idan suka tashi rikicin su.

” Sannan tun ranar da maidakin Adetsay ta fatattake mu da wuka da da muka je rabon fada muka fita harkansu wanda hakan ya sa muka kasa gane dalilin wannan rikici wannan karo.

Yamu ya ce sun gana da shugaban karamar hukumar Makudi Akange Audu inda ta tabbatar musu da hakan.

Share.

game da Author