Masu gadin babbar daffon matattarar rumbunan man fetur ta NNPC da ke Maiduguri sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin biyan su albashin watanni 7 da ba a yi ba.
Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito cewa masu boren sun datse kofar shiga daffon domin hana kowa shiga ciki.
Sun kuma hana tankokin dakon mai masu loda mai su shiga ko su fita cikin harabar daffon.
Masu gadin, wadanda ke karkashin JAFI Security Limited, sun rika daga kwalaye da kyallayen da suka yi wa rubuce-rubuce da suka hada da : “A biya mu albashin mu na wata bakwai”, “Mu fa ba bayin ku ba ne”, da kuma “An koro ‘ya’yan mu daga makaranta.”
Daya daga cikin masu zanga-zangar, mai suna Iliya Miyem, ya nuna rashin jin dadin yadda aka ki biyan su hakkin watanni bakwai, duk kuwa da rokon da suke ta yi a biya su tun tuni.
“A shekarun baya rabin albashi ake biyan mu, a cikin wannan shekarar kuma, sai aka daina biyan mu gaba daya. Rabon da a biya mu rabin albashin ma tun daga watan Afrilu.”
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati ta shiga cikin lamarin.
Wasu masu boren da suke hada da Ali Bura da Umar Ali, duk sun maimaita irin ikirarin da Miyem ya yi na rashin biyan su albashin.
Sun kuma yi nuni da cewa rashin su albashin ya jefa su da iyalan su a cikin halin matsi, kuncin rayuwa da takaicin rashin iya biyan bukatun yau da kullum.
Ali ya zargi mahukuntan kamfanin da yin watsi da matsalar da aka jefa su. Ya ce sau da dama a baya a duk lokacin da suka yi korafin rashin biyan su albashi, sai a yi musu barazanar korar su daga aiki.
Sauran wadanda aka yi hira da su sun bayyana halin kuncin da su ke ciki su da iyalan su, wasu kuma suka bada labarin yadda aka koro ‘ya’yan su daga makaranta saboda sun kasa biyan kudin makarantar su.
Sai dai kuma Manajan Riko na daffo din mai suna Nasiru Gaji, ya ki ya yi magana, kuma ya bada umarnin a kori ‘yan jarida daga farfajiyar daffo din.
“Ku fice ku bar wurin nan, idan ba haka ba kuma zan sa a yi biji-biji da ku. Idan ba ku fice nan da minti daya ba, zan sa a kame ku.
“’Yan jarida ba s u da iznin da za su dauki hotuna a wurin nan.” Inji Gaji.
Jiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton musamman a kan yadda bashi ya rike wa kamfanin NNPC wuya, har ta gai ga kamfanin ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasikar rashin kudin da ai rika shigo da mai daga kasasshen waje.
Wannan ne ya sa aka kwashi dala bilyan 1.5 daga asusun NLNG aka bayar ramce ga NNPC, kudaden da har yau su ne ake jalautawa ana sayo tataccen fetur daga waje.
Discussion about this post