Malaman jami’o’in Najeriya sun fara yajin

0

Ben Ugwoke na jami’ar Abuja ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa kungiyar malaman jami’o’in kasar nan sun fara yajin aiki na bai daya da basu da ranar janye wa.

Kungiyar malaman ta ce ta fara yajin aikin ne a dalilin kin rashin biya wa malaman jami’o’i bukatun su kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi alkawari.

Malaman jami’o’in sun koka kan burus da gwamnati ta yi da su cewa gaba daya jami’o’in kasar nan ba za su ci gaba da aiki ba sai wada ta yiwu.

Wasu daga cikin bukatun kungiyar sun hada da rashin wadata jami’o’in da kudade domin gudanar da ayyukan su, sannan kuma da rashin maida hankali da gwamnati bata yi ba ga harkar ilimin jami’o’i a kasar nan.

Share.

game da Author