Majalisar Dinkin Duniya ta kashe Dala miliyan 70 wajen tallafa wa ‘yan gudun hijira a Arewa Maso Gabashin Najeriya

0

Ofishin kula da aiyukkan jinkai na majalisar dinkin duniya (COHA) ta bayyana cewa ta kashe akalla dala miliyan 70 wajen tallafa wa ‘yan gudun hijiran dake yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Ofishin ta ce duk da haka ‘yan gudun hijira miliyan bakwai na nan a Najeriya da ke matukar bukatan agaji saboda aiyukkan Boko Haram.

Jami’ar COHA Samantha Newport ta bayyana haka wa manema labarai a garin Legas.

Samantha ta ce domin tallafa wa wadannan mutane ne ya sa ta bude wani asusu mai suna ‘Nigerian Humanitarian Fund (NHF) domin tara kudaden da za a bukata don wannan aiki.

” Mun tara dala miliyan 70 a cikin wannan asusun ta hanyar gudunmawa daga kasashen Sweden, Germany, Netherlands, Denmark, Belgium, Norway, Ireland, Switzerland, Korea, Iceland, Canada, Spain, Luxembourg, Malta, Azerbaijan da Sri Lanka.

” A yanzu haka mun kashe wadannan kudade wajen samar da abinci, ruwa sha, magunguna da wuraren kwanciya a sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin.

Share.

game da Author