Shugaban kungiyar likitoci na NAjeriya (NMA) Francis Faduyile ya bayyana cewa kungiyar sa ta amince ta hada kai da hadaddiyar kungiyoyin ma’aikatan jinya domin ci gaban fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Faduyile ya fadi haka ne a taro da kungiyar likitoci ta yi da hadaddiyar a kungiyoyin ma’aikatan jinya na kasa (NANNM) a Abuja ranar Talata.
” Rashin jituwar da ke tsakanin mu ya samo asali ne tun bayan nunawa kakara da muka yi da kada gwamnati ta kara wa ma’aikatan jinyar albashi. Hakan ya sa mun yi ta kai ruwa rana a tsakanin mu amma yanzu mun warawre wadannan matsaloli da ta dabaibaye mu domin ci gaban fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Da yake jinjinawa wa shugaban kungiyar likitocin shugaban kungiyar NANNM Abdrafiu Adeniji ya bayyana cewa lallai za su hada hannu don ganin irin wannan matsala bai sake shiga tsakanin su ba.