Shugaban karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara Awwal-Bawa Moriki ya bayyana cewa zai bada sakamako mai tsoka da ya kai Naira miliyan biyar ga duk wanda yake da bayanan da zai taimaka wajen gano tagwayen da aka sace tun a watan Oktoba a jihar.
Moriki ya fadi haka ne da yake ganawa da manema labarai a Zurmi ranar Talata.
Idan ba a manta ba a watan Oktoba ne wasu masu garkuwa da mutane suka sace Hassana da Hussaina a garin Dauran.
Bayanai sun nuna cewa masu garkuwan sun sace wadannan tagwaye ne a lokacin da suka fito raba katin gaiyatan bukin auren su.
Moriki ya hori mutane da su ci gaba da addu’o’I domin gano wadannan ‘yan mata da ceto su daga wadannan miyagu.