Jami’an Kwastam sun harbe wani dan fasa-kwauri a lokacin suka yi kokarin kwace wata mota da aka yi sumogal din ta cikin Najeriya, wadda ke da fenti launin sojoji.
Nan da nan jami’an kwastam din suka yi nasarar kama motar, wadda ta sojoji ce da aka shigo da ita ta kan iyakar Ebute a kan hanyar Ilaro-Oja, kan iyakar Karamar Hukumar Yewa ta Kudu da ke cikin Jihar Ogun.
Kakakin Kwastam na Jihar Ogun, Abdullahi Maiwada, shi ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Laraba, a cikin wata takardar da ya raba musu.
Ya ce an kama motar sojojin ce bayan an tsegunta wa jami’an kwastan cewa an shigo da motar.
Sai dai kuma ya kara da cewa jami’an kwastan sun gamu da tirjiya jama’ar gari, domin sun yi kokarin haka a kama motar.
Ya ce jama’a sun yi gangami inda suka tare hanyar da kwastan za su wuce, suka rika jifar jami’an kwastan din da duwatsu, kwalabe, adda, sanduna da sauran makaman da hannu zai iya dauka ya sarrafa.
“Ganin yadda motar ta ke da barazana ga tsaron kasar nan, tunda ta sojoji ce, sai jami’an kwastan suka nemi a karo musu taimakon zarata. Wannan ya haifar da bude wuta, har harsashi ya samu daya daga cikin tsageran da suka datse hanya, ya mutu.”
Amma yanzu komai ya wuce, kowa ya ci gaba da harkokin sa a yankin.
Shugaban Kwastan na jihar ya hori jama’a da su daina daure wa masu fasa-kwauri gindi.