Shugaban Hukumar Kwastan na Kasa Hameed Ali, ya bayyana cewa jami’an sa sun kama kwantina har guda 40 makare da kwalaben taramol.
Ali ya bayyana haka a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi a Lagos dangane da kwayoyi da ruwan magungunan da kwastam suka kama, ciki har da taramol.
Ya ce jami’an kwastan sun samu nasarar wannan gagarimin aiki ne ta hanya kara matsa kaimin sa-ido da kuma taimakon Hukumar Hana Tu’ammali da Da Muggan Kwayoyi, watau NDLEA.
Ali ya nuna damuwar sa a kan yadda wasu marasa kishi a kasar suka rufe ido sai sun yi kudi ta hanyar safarar muggan kwayoyi, duk kuwa da sun san mummunan illar su ga jama’a.
Ya ce za a gudanar da kwakwaran bincike kan wadanda suka shigo da taramol da kuma kudaden da suka nemi bayarwa a matsayin cin hanci.
Shugaban na kwastam ya kara da cewa jami’an sa da ke tashar ruwa ta Apapa ta kama jirgin sama biyu da helikwafta daya, wadanda aka yi kokorin sumogal din sau wajen kasar nan, daga nan gida Najeriya